Sojojin Isra’ila sun dauki wasu Yahudawa da dama ‘yan asalin kasar Yemen aiki, wadanda ke magana da harshen Larabci a cikin yaren Yemen, don taimakawa wajen yaki da ‘yan Houthis a Cewar wakilin kamfanin watsa Labarai na Isra’ila
A wani rahoto da At-tajdid News ta samu daga majiyarta ta yankin gabas ta tsakiya Isra’ila za ta kasance a Gaza na dogon lokaci bayan rantsar da Trump sannan matsin lambarta zai cigaba da karuwa.
A wani fifan Video da kafar yadda labarai ta Aljazeera, ta bayyana Sakataren harkokin wajen Amurka yana ganin fatan samun dauwamammen zaman lafiya a Lebanon tare da janyewar sojojin Isra’ila daga yankin.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta yi Allah wadai da watsi da zargin da ake yi mata da kuma zargin Isra’ila game da fadada taswirarta kamar yadda suka fitar, wanda hakan ke nuna sassan kasashen Larabawa (Jordan, Lebanon, da Siriya) a cikin iyakokin da ake zarginsu da mamaya.
Mai rahoto;
M.B.Gama.




