By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Sami Tirjiya Mai Tsanani Tsakanin Dakarun Hezbollah da sojojin Isra’ila  a Lebanon
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > An Sami Tirjiya Mai Tsanani Tsakanin Dakarun Hezbollah da sojojin Isra’ila  a Lebanon
International News

An Sami Tirjiya Mai Tsanani Tsakanin Dakarun Hezbollah da sojojin Isra’ila  a Lebanon

Attajdid
Last updated: 2024/10/22 at 9:28 PM
Attajdid Published October 22, 2024
Share
SHARE

Mayakan Hezbollah sun gwabza kazamin fada da sojojin kasa na Isra’ila a kan iyakokin kasar guda uku a kudancin kasar Lebanon, kamar yadda kafafen yada labaran kasar Labanon suka bayyana.

 

Kafar yada labaran ta ce sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan Aita al-Shaab, Qaouzah da Ramiya da manyan bindigogi.

 

A gefe guda kuma, wata yarinya ‘yar kasar Lebanon ta mutu sakamakon raunukan da ta samu a wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai a garin Kharayeb da ke gabashin kasar Lebanon, kamar yadda NNA ta ruwaito.

 

An kuma bayar da rahoton wasu hare-hare ta sama da dama a garuruwan Kharayeb, Houmine El Faouqa, Jarjouaain, Habbouch da kuma Arab Salim da ke kudancin kasar Lebanon.

 

Lebanon ta ce harin da Isra’ila ta kai a babban birnin Baalbek da ke gabashin kasar ya kashe mutum shida ciki har da wani yaro, yayin da kafafen yada labarai na kasar suka rawaito cewa harin ya afkawa wani gini da ke wani yanki mai cike da cunkoso.

 

“Harin da makiyanmu Isra’ila suka kai…a Baalbek ya kashe mutane shida, ciki har da wani yaro,” in ji ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon, kuma kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa dukkan mutanen shida ‘yan gida daya ne.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 22, 2024 October 22, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kasa Super Eagles wacce ta ƙunshi zallan yan wasan da ke taka leda a Najeriya, tayi rashin nasara a wasan ta na farko na gasar cin kofin tamaula na ƙasashen nahiyar Afrika a hannun takwararta na ƙasar Senegal da ci daya da nema. Manazarta al’amurra wasan ƙwallon ƙafa na kallon rashin nasara a matsayi wata yar manuniya da ke nuna irin koma-baya da kuma siyasa da ta dabaibaye al’amurran zaɓen yan wasa da zasu wakilci Najeriya a wannan gasa. Alal misali, da dama daga cikin manazarta da suka kalli wasan sun nuna damuwa kan yadda masu ruwa da tsaki suka ajiye shahararren ɗan wasan Kano Pillarss Rabiu Ali Pele bisa hujjar shekarun haihuwa duk da cewa yana kan ganiyyar sa na wasa a gasar Firimiya Lig ta ƙasa, hasali ya kasance ɗan wasa daya tilo da ya kafa tarihin cin mafi yawan kwallayeya gasar ta Firimiya Lig. A sauran wasan gasar da aka fafata a rukunin da Najeriya ke ciki, an tashi daga wasa kowacce ƙungiya na da ci daya tsakanin Congo da Sudan, abin da ke nuni da cewa zuwa yanzu Najeriya ce ta karshe rukunin na ‘D’, kuma Ƙungiyoyi biyun da suka fi yawan maki sune zasu haura zuwa zagaye na gaba na gasar. A wasannin da za’a fafata a wannan rana, Burkina Faso za ta kara da jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, sai kuma wasa tsakanin Mauritania da Tanzania. A wani labarin kuma, Wata kotu a Ingila ta bayar da belin tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey bayan tuhumar sa bisa zargin laifukan cin zarafin wasu mata. An zargi ɗan wasan na Ghana da yi wa wasu mata biyu fyaɗe tare da cin zarafin wata daban. Lamarin da ake zargi ya faru ne a tsakanin shekara ta 2021 zuwa 2022 lokacin da yake taka leda a Arsenal. Daga cikin hukunce-hukuncen da kotun ta yanke masa, ta hana Partey yi wa kowace daga cikin matan magana, sannan dole ya sanar da ƴansanda idan zai canja gida ko zai yi

Attajdid Attajdid August 6, 2025
INTERNATIONAL DAY OF MENSTRUAL HYGIENE: “Exposing an age old stigma deeply rooted in our traditions”.  
Mayaƙan Boko Haram Sun Miƙa Wuya ga Sojojin Nijeriya
Germany withdraws troops from Niger Amidst Of Gaza Genocide
Zulum ya jaddada kudirinsa na sake tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?