Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kasa Super Eagles wacce ta ƙunshi zallan yan wasan da ke taka leda a Najeriya, tayi rashin nasara a wasan ta na farko na gasar cin kofin tamaula na ƙasashen nahiyar Afrika a hannun takwararta na ƙasar Senegal da ci daya da nema.
Manazarta al’amurra wasan ƙwallon ƙafa na kallon rashin nasara a matsayi wata yar manuniya da ke nuna irin koma-baya da kuma siyasa da ta dabaibaye al’amurran zaɓen yan wasa da zasu wakilci Najeriya a wannan gasa.
Alal misali, da dama daga cikin manazarta da suka kalli wasan sun nuna damuwa kan yadda masu ruwa da tsaki suka ajiye shahararren ɗan wasan Kano Pillarss Rabiu Ali Pele bisa hujjar shekarun haihuwa duk da cewa yana kan ganiyyar sa na wasa a gasar Firimiya Lig ta ƙasa, hasali ya kasance ɗan wasa daya tilo da ya kafa tarihin cin mafi yawan kwallayeya gasar ta Firimiya Lig.
A sauran wasan gasar da aka fafata a rukunin da Najeriya ke ciki, an tashi daga wasa kowacce ƙungiya na da ci daya tsakanin Congo da Sudan, abin da ke nuni da cewa zuwa yanzu Najeriya ce ta karshe rukunin na ‘D’, kuma Ƙungiyoyi biyun da suka fi yawan maki sune zasu haura zuwa zagaye na gaba na gasar.
A wasannin da za’a fafata a wannan rana, Burkina Faso za ta kara da jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, sai kuma wasa tsakanin Mauritania da Tanzania.
A wani labarin kuma, Wata kotu a Ingila ta bayar da belin tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey bayan tuhumar sa bisa zargin laifukan cin zarafin wasu mata.
An zargi ɗan wasan na Ghana da yi wa wasu mata biyu fyaɗe tare da cin zarafin wata daban.
Lamarin da ake zargi ya faru ne a tsakanin shekara ta 2021 zuwa 2022 lokacin da yake taka leda a Arsenal.
Daga cikin hukunce-hukuncen da kotun ta yanke masa, ta hana Partey yi wa kowace daga cikin matan magana, sannan dole ya sanar da ƴansanda idan zai canja gida ko zai yi tafiya ƙasar waje.
Mai shekara 32 ya ce ya amince da hukuncin da kotun ta yanke.
Partey zai sake gurfana a gaban wata kotu a Ingila ranar 2 ga watan Satumba kan wannan zargin.
Mai Rahoto
Nura Abubakar Musa




