By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Isra’ila Ta Cigaba Da Ruwa Bama-bamai Kan Fararen hula A Gaza
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Isra’ila Ta Cigaba Da Ruwa Bama-bamai Kan Fararen hula A Gaza
International News

Isra’ila Ta Cigaba Da Ruwa Bama-bamai Kan Fararen hula A Gaza

Attajdid
Last updated: 2024/09/02 at 5:12 PM
Attajdid Published September 2, 2024
Share
SHARE

A yaƙin da Isra’ila ta kwashe kwana 332 tana yi a Gaza ta kashe Falasɗinawa fiye da 40,738 yawancinsu mata da yara sannan ta jikkata mutum fiye da 94,154, kuma ana da tabbacin mutum 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da ta rusa.

Ma’aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, yayin da Isra’ila ke barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin.

A ranar Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024 dakarun Isra’ila sun kashe fararen-hula biyu tare da jikkata wasu bayan sun jefa bama-bamai a wani gida da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA.

Rundunar kare fararen-hula ta yankin ta ce ta ɗauko gawawwaki guda biyu da kuma mutanen da suka jikkata daga gidan iyalan Araj da ke Jalaa Street bayan Isra’ila ta kashe su.

Daga bisani adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 11 bayan jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a Makarantar Safad da ke kudu maso gabashin Gaza, inda ‘yan gudun hijira suka sami mafaka.

Ma’aikatan ceto sun ci gaba da gudanar da aikin tono wasu mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, yayin da Isra’ila ke barazanar ci gaba da kai hare-hare a yankin.Ministan harkokin wajen Saudiyya na yunƙurin ganin an daina kai hare-hare a Gaza.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na Turkiyya, Masar, Jordan, Bahrain da Gambia ranar Lahadi a yunƙurin ganin Isra’ila ta daina kai hare-hare a Gaza da kuma bai wa Falasɗinawa ‘yanci.

Bin Farhan ya yi magana da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan game da bayanai na baya-bayan nan halin da Falasɗinawa suke ciki, inda ya mayar da hankali kan yunƙurin ƙasashen Musulmai na ganin sun maido da martabar Falasɗinawa da kuma haɗa-kai don kawo ƙarshen hare-hare da keta hakkin da Isra’ila take yi wa Falasɗinawa.

Da yake tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty, ya mayar da hankali kan halin da yankunan Falasɗinawa suke ciki da kuma buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin dakatar da rashin mutuncin da Isra’ila take yi wa Falasɗinawa, yayin da kuma ya jaddada buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta.

Kazalika a yayin da yake magana da Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya bayyana buƙatar gagauta tsagaita wuta da kuma haɗin-kan dukkan ƙasashen Larabawa da na Musulmai wajen ganin an yi wa Falasɗinawa adalci, ciki har da ƙirƙiro musu ƙasa mai cin gashin kanta.

A cewar majiyarmu daga ‘yankin gabas ta tsakiya.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 2, 2024 September 2, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News

Menene Manufar Halittar Dan Adam a bayan kasa

Attajdid Attajdid July 18, 2024
Jam’iyyar NNPP ta Lashe Zaɓen Shugabannin ƙananan Hukumomin 44 da Kansiloli 484 Jihar Kano: Farfesa Malumfashi.
JUST IN: Tension as fire guts Emir Sanusi’s palace in Kano
Matsananciyar Zanga-Zanga ta Barke a Isra’ila
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da sakon ta’aziyya a kasar Ghana
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?