NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce ta cafke wani mai suna Muhammad Abubakar da aka fi sani da suna Bello Karama da wasu mutane biyar da su ka yi kaurin suna wajen sanya muggan Kwayoyi a kayan matafiya a filin Jiragen Sama na Malam Aminu Kano.
Daraktan Hulda da Jama’a na hukumar NDLEA Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a Abuja inda ya ce an cafke wadanda ake zarginne ne bayan da aka gano cewa su na da hannu a turawa da haramtattun kwayoyi a cikin kayayyakin ‘Yan Nigeria da ke tafiya aikin umara kasa mai tsarki inda a birnin Jedda aka tsare su abisa zarginsu da safarar kwaya.
A cewar Babafemi bayan an tsare maniyyatan su uku a birnin Jedda ya sanya Iyalansu anan Nigeria su ka shigar da korafi ga hukumar ta hana sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa NDLEA, inda kuma shugaban hukumar Birgediya Muhammad Buba Marwa Mai Ritaya ya ba da umarnin a gudanar da Bincike har kuma aka bankado su.
Hukumar ta ce ‘Yan Nigeria mutum ukun da aka tsare a saudiyya sun hadar da Maryam Abdullahi da Abdullahi Aminu da kuma Abdulhamid Saddiq wadanda su ka bar nan Kano ta Jirgin Saman Ethiopian Airline a ranar 6 ga watan Augusta domin zuwa aikin umara kasar Saudiyya inda su ka bi ta Addis Ababa wanda acan ne aka kara musu Jakankuna guda shida wadanda ba na su ba ne kuma a cikin uku daga ciki akwai haramtattun kwayoyi.
Sanarwar ta hukumar NDLEA ta ce wadanda ake zargin su na a karkashin kulawar hukumar a Abuja inda ake cigaba da bincike.




