Kotun kolin Ghana ta yi watsi da hukuncin da kakakin majalisar dokokin ƙasar ya yanke a ranar 17 ga watan Oktoba, da ya kori wakilai huɗu daga majalisa.
Kotun kolin ta ce hukuncin da kakakin majalisar ya yanke ya saɓa wa kundin tsarin mulki, inda a ranar 7 ga watan Nuwamba 2020 ya ayyana kujerar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Fomena a matsayin babu mai ita bayan ficewar ɗan majalisar daga jam’iyya mai mulki ta NPP.
Wannan hukunci dai ya ba da damar komawa ci gaba da zaman majalisar bayan shafe makonni na rashin tabbas da kuma ɗage zaman tattaunawa da aka yi kan lamarin.
Shugaban ɓangaren masu rinjaye da ya kai batun gaban kotu ya ce “wannan lokaci ne da kowa zai fito don nuna goyon baya ga tsarin dimokraɗiyya wanda ke buƙatar ladabi wanda shi ne hanyar da jam’iyyar NPP mai rinjaye ta bi don tabbatar da cewa mun yi komai bisa doka.”
“Muna sa ran takwarorinmu na ɗaya ɓangaren ciki har da shugaban majalisar za su mutunta sakamakon wannan shari’a don kai ƙasa gaba,” in ji shi.
Babban attoni janar na ƙasar Ghana Godfred Yeboah Dame ya shaida wa manema labarai cewa “a duk lokacin da kotu ta yanke hukunci, tana da cikakken tsari kuma dole ne a mutunta matakin da ta ɗauka.”
Aika, Kotun kolin Ghana ta yi watsi da hukuncin da ya kori wakilai huɗu daga majalisa
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu




