Larabawa suna kiran wannan kasa da “Suriyah”, yayin da turawa suke cewa “Siriya”. Kasa ce daga cikin kasashen Larabawa na Gabas ta tsakiya. Kasar bangare ce ta wata babbar kasa da aka sani a cikin tarihi da “Yankin Sham” da larabci, ko kuma “The Levant” da turanci. Turawa ne suka raba wannan babban yankin zuwa kasashen hudu – Suriyah, Lubnan ko kuma Lebanon, Urdun ko kuma Jordan da kuma Falastin.
An samar da kasar Suriyah bayan gama yakin duniya na daya, a shekarar 1920. Ta fara ne da mulkin sarauta, daga baya faransawa suka kwace ta, suka yi mata mulkin mallaka.
Kasar Suriyah tana da mutane kimanin miliyan ashirin da biyar, kusan kashi casa’in cikin dari nasu Larabawa, kashi tara kurdawa, kashi daya sauran kabilu kamar turkamenawa.
Kusan kashi tamanin da bakwai cikin dari na mutanen kasar musulmi ne, kashi goma kirista, kashi uku kuma ‘yan duruz, su kamar mutum 500,000.
Daga cikin musulmin kashi 74% Sunni ne, kusan 10% ‘yan shi’ar Nusairiyya Alawiyya, sauran kashi ukun kuma ‘yan shi’ar imamiyya da isma’iliyya.
Lokacin da faransawa su ke mulkin mallaka, saboda tsari irin nasu na kokarin danne wadanda suka fi yawa sai suka dauki Alawiyyawan can da ba su wuce kashi goma cikin dari ba suka cika su a cikin soja da makarantun boko.
Alawiyyawa wasu mutane ne da suka balle daga shi’a imamiyya isnaa ashriyya irin ta Iran da Irak da Lebanon. Da suka balle sai suka kirkiro sabbin akidu da bidi’o’i, suke cewa Allah ne ya sauka a cikin jikin Sayyiduna Aliyu, kuma shi Aliyun shine ya aiko Annabi Muhammad (saw). Suke cewa babu wata kiyama ko Aljanna ko wuta. A wurin su duk wanda ya mutu ya kan dawo duniya ne a cikin sabon jiki a sake haihuwar shi. Suka kuma ce duk ibadodi da suka hada da Sallah da Zakkah da Hajji ba dole ne ba, don haka ba su yi. Ba su karanta Alkur’ani, ba su da Masallatai sai dai wasu dakunan bauta inda giya babban ginshiki ce a ibadar tasu.
Su kansu ‘yan shi’a imamiyya isnaa ashriyya sun dauki ‘yan Nusairiyya Alawiyya ba su cikin musulunci. Zuwan Kumaini ne ya yi kokarin hada kai da su.
To wadannan su ne faransawa suka sa gaba, sama da musulmi Sunni mafi yawa a Suriyah.
Da Jamal Abdun Nasir ya kwaci mulkin Masar sai ya fito da wata jam’iyya ta gurguzu da ke bin Tafarkin Rasha, mai suna “Jam’iyyar Ba’ath”, watau Jam’iyyar farfadowa ko kuma falkawa. Manufofin wannan jam’iyya sune: hada kan dukkan kasashen Larabawa a bisa kishin kabilanci da ajiye addini gefe daya, da kuma daukar tsarin tattalin arziki irin na gurguzu (Ishtirakiyyah) wanda dukkan harkokin kasuwanci suna hannun gwamnati ba ‘yan kasuwa ba. Da wannan Abdun Nasir ya yi kokarin hado kan kasashen Larabawa su zama kasa daya.
Kasashen Larabawa da dama sun karbi Jam’iyyar Ba’ath daga Abdun Nasir, kamar ita Suriyah da Irak karkashin Saddam da Libya karkashin Gaddafi da Tunisiya karkashin Bargiba.
Sojojin Suriyah, wadanda mafi yawansu alawiyya ne su ne suka karbi Jam’iyyar Ba’ath, suka yi juyin mulki suka karbi gwamnati. Da haka hukumar Suriyah ta dauki kishin kabilancin larabci da fada da addini da tsarin tattalin arzikin gurguzu (Ishtirakiyyah) da kuma cikakkiyar hulda da kasar Rasha.
A shekarar 1973 Hafiz Assad, wanda babba ne a cikin gwamnatin sojan Suriyah ya jagoranci wani juyin mulki ya zama shugaban kasa, har wala yau dai a karkashin Jam’iyyar Ba’ath, kuma shima dan Alawiyya ne. Hafiz Assad nan take ya cika gwamnatinsa da ‘yan Alawiyya ‘yan uwanshi, inda kashi 75% na sojoji da ‘yan sanda da jami’an tsaron asiri da ma’aikatan gwamnati suka wayi gari duk ‘yan Alawiyya ne, wadanda mafi rinjayen mutanen kasar ke ganin su a matsayin kafurai.
A takaice dai mulkin Hafiz Assad ya kawo wa mafi rinjayen musulmi Sunni na Suriyah tsarin mulkin da suke gani na kafurci ne kala biyu: tsarin gurguzu na Ba’ath da kuma mulkin danniya na ‘yan Alawiyya.
Tun daga lokacin malamai da kungiyoyin addini na Sunnah suka fara kalubalantar wannan al’amari. Wadanda suka shiga gaba cikin wannan kalubale sune kungiyar Ikhwanul Muslimun.
A shekarar 1982 an samu wata arangama tsakanin Ikhwanul Muslimun da shugabannin Jam’iyyar Ba’ath a birnin Hama, birni na hudu mafi girma a kasar Suriyah. Sakamakon haka Assad ya tura wa garin sojoji karkashin wani kaninsa, inda aka rusa kashi biyu cikin uku na garin, aka kashe fiye da mutum dubu arba’in.
Haka Assad ya ci gaba da mulkin danniya da kama karya mai tsanani na ma’abota addininsa har zuwa mutuwarsa a shekarar 2000. Kafin mutuwarsa sai da ya tabbatar cewar dansa Basshar Assad shine zai gajeshi. Shima Basshar ya ci gaba da tsarin ubansa ba tare da canja komai ba, su kuma malamai da kungiyoyin Sunnah sun ci gaba da gwagwarmayar neman canji da ‘yanci. Ana hakan ne guguwar neman sauyi da ake kira “Rabi’ul Arabi ” ta kada a cikin kasashen Larabawa a shekarar 2011.
Zamu kammala a darasi na gaba in sha Allahu.
Modibbon Gusau.
8/6/1445
10/12/2024.




