By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a sake fasalin tsarin ilimi don ya zo daidai da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban zamani
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a sake fasalin tsarin ilimi don ya zo daidai da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban zamani
News

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a sake fasalin tsarin ilimi don ya zo daidai da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban zamani

Attajdid
Last updated: 2024/11/23 at 4:51 PM
Attajdid Published November 23, 2024
Share
SHARE

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a yi cikakken nazari kan tsarin ilimi na Najeriya don daidaita alaka tsakanin cibiyoyin ilimi da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban kasa.

 

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a yayin wata ziyarar ban girma da Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar Kula da Lamuni ta Ilimi ta Najeriya (NElfund) Mista Akintunde Sawyerr ya kai a fadar gwamnati, Maiduguri.

Gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa cewa yawancin daliban da suka kammala karatun digiri da manyan cibiyoyi ilimi suka yaye ba su da kwarewar da suka dace don kyankasa sabbin dabarun kere’kere da abubuwa da ci gaban fasaha.

 

Ya bukaci gidauniyar Nelfund da ta yi nazari sosai kan batun tare da aiwatar da hanyoyin da za su baiwa masu digiri damar zama masu dogaro da kansu maimakon jiran aikin gwamnati.

 

“Muna da manyan matsaloli guda biyu a tsarin iliminmu: rashin daidaito tsakanin cibiyoyin ilimi da masana’antu, saboda ba sa sadarwa yadda ya kamata, da rashin daidaito tsakanin kasuwar kwadago da wadanda suka kammala karatun digiri, wadanda da yawa daga cikinsu ba su da shiri don yin aiki a masana’antu,” in ji Zulum.

 

Zulum ya bukaci Nelfund da ta tallafawa tsarin ilimin kasuwanci, fasaha, da sana’oin hannu.

 

Ya kara da cewa, “Bayan bayar da lamuni, ina roƙon ku da ku bincika hanyoyin da za ku tallafa wa ilimin kasuwanci da haɓaka horar da fasaha da sana’o’i don rage ƙin yarda da waɗannan mahimman fannonin karatu,” in ji shi.

 

Gwamnan ya yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa kafa Nelfund, yana mai jaddada cewa samar da gidauniyar zai rage jahilci da karacin ilimi a musamman a yankin Arewa maso Gabas.

 

Ya yi alkawarin zaburar da shugabannin kananan hukumomi da sarakunan gargajiya don wayar da kan jama’a game da shirin, inda ya yi nuni da muhimmancinsa ga daliban da ba su da galihu da ke son neman ilimi.

 

“Na tattauna da shugabannin manyan makarantu tun lokacin da kuka hau kan karagar mulki, kuma rahotanni sun nuna cewa yawancin daliban da suka nemi lamunin Nelfund sun karbe su cikin sauki,” in ji Zulum.

 

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Asusun Lamuni na Ilimi na Najeriya (NElfund), Mista Akintunde Sawyerr, ya bayyana manufar asusun na magance matsalar karuwar daliban da suka kasa cigaba da karatu saboda matsalar kudi.

 

Ya lura cewa lamunin ba shi da kudin ruwa, tare da biyan kuɗi a kashi 10% na abin da mai karɓa ya samu bayan samun aikin yi.

 

Mista Sawyerr ya samu rakiyar mataimakin shugaban jami’ar jihar Borno, Farfesa Babagana Gutti, da wakilan kungiyar daliban Najeriya ta kasa (NANS).

 

Dauda Iliya

Mai Baiwa Gwamnan Jihar Borno Shawara

(Harkokin Yada Labarai kuma Mai Magana da Yawun sa)

 

Mai rahoto;

Abdullahi Mustapha.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid November 23, 2024 November 23, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Yankin Nijar yana Fama da Hare-haren ‘Yan Ta’adda

Attajdid Attajdid September 19, 2024
ABIBATI TINUBU MEMORIAL QUR’ANIC RECITATION COMPETITION: A CELEBRATION OF MOTHERHOOD, FAITH, AND LEGACY
Wakilan Kasashan Afarka Sunyi Kausasan Bayanai a Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo na 79
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Hare-hare ta sama da Isra’ila ke kai wa sun fi razana ni’
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?