Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
A shekarar 2023 Hilda ta shiga kundin bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girki.
Kafin a tabbatar da cewa ta kafa tarihi, har sai kundin Guinness World Record ya tantance girkin da ta yi.
Jollof rice ko kuma dafa-dukar shinkafa abinci ne da ake sha’awa sosai a yankin Yammacin Afirka, inda ƙasashe kamar Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambiya ke da’awar cewa su ne ke da mafi kwarewa a wurin girka ta.
Mai rahoto
Mustapha Garba Usman




