- An kashe wani fitaccen jagoran Falasɗinawa Ziad Abu Hlail yayin wani samame da Isra’ila ta kai gidansa don kama ɗaya daya daga ‘ya’yansa a unguwarsu Dura, a arewacin Hebron a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye. Ana yawan ganinsa yana tunkarar sojojin Isra’ila a bidiyoyinsa da ake wallafa wa a kafofin sada zumunta yana hana sojojin Isra’ila yin harbi ko kama Falasɗinawa matasa.
Iyalan Abu Hlail mai shekara 66 sun ce sojojin Isra’ila sun yi dirar mikiya a gidansa yayin wani samame da suka kai tsakar dare, suka sa ya sa ya faɗi lokacin da ya tafi duba ɗansa da aka tsare.
Ya suma sannan ya mutu a gidansa kafin motar ɗaukar marasa lafiya ta kai shi asbiti, kamar yadda matarsa Basma Abu Hlail ta bayyana.
“Muna bacci wajen 4:00 na asuba sojoji (na Isra’ila) sun kewaye gidanmu suka kama ɗana, sun fitar da shi daga gidan. Mahaifinsa ya so ya bi bayansa da gudu, amma ba su bar shi ba. Sun tura ƙofa, sai ya faɗi ya mutu. Ya yi shahada. Mun kira motar ɗaukar marasa lafiya amma ba ta zo ba. Allah ya ɗauki ransa a gida, motar ɗaukar marasa lafiyar ba ta ɗauke shi zuwa asibiti ba,” a cewar matarsa.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




