By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami’o’in ‘Yan Koran Yahudawan sahyoniyya 
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami’o’in ‘Yan Koran Yahudawan sahyoniyya 
International News

Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami’o’in ‘Yan Koran Yahudawan sahyoniyya 

Attajdid
Last updated: 2024/10/15 at 1:34 PM
Attajdid Published October 15, 2024
Share
SHARE

Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan ya Bayyana Fishinsa Kan Jami’o’in ‘Yan Koran Yahudawan sahyoniyya 

 

“Babu tantama cewa ‘yan koren Isra’ila ne ke riƙe da iko da manyan jami’o’in duniya da sunan bayar da tallafin kuɗi,” in ji shugaban Turkiyya.

 

Ta’annatin da Isra’ila ke aikatawa a yankin Gaza na Falasɗinu ya bayar da gudunmawa wajen fitowa fili a fahimci yadda ‘yan koren Isra’ila ke da iko kan manyan jami’o’in duniya, in ji shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

 

“Mun shaida irin wannan abin kunyar inda ‘yan sanda suka dinga musguna wa ɗaliban da suka ce ‘ana aikata kisan kiyashi a Gaza’, shugaba Erdogan ya bayyana haka a ranar Talata a yayin taron sabuwar shekarar karatu ta 2024/2025 a Ankara.

 

Ya kuma ja hankali kan yadda aka tursasawa shugabannin jami’o’i da suka bayar da damar yin zanga-zangar adawa da kisan Falasɗinawa yin murabus, aka azabtar da su tare da titsiye su a gaban majalisar dokokin Amurka.

 

Ya jaddada cewa “Babu wani suka ko bayyana ra’ayi game da Falasɗinawa aka yarda da shi. Ya zama babu tantamar cewa ‘yan koren Isra’ila ne ke riƙe da iko da manyan jami’o’in duniya inda suke fakewa da bayar da tallafin kuɗaɗe.”

 

Shugaban na Turkiyya ya kuma soki gwamnatocin ƙasashen Yammacin duniya bisa gazawa wajen kawo ƙarshen kisan kiyashi a Gaza tsawon shekara guda, yana mai cewa sun zubar da ƙimarsu “a ƙoƙarin da suke yi na kare Isra’ila”.

 

Yaƙi da dukkan ‘yan adam

 

Da take ci gaba da saɓawa matakin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauka na kiran da a tsagaita wuta a Gaza, Isra’ila na ci gaba kai munanan hare-hare Gaza, tana mai fakewa da harin da ƙungiyar tirjiya ta Falasɗinawa Hamas ta kai mata a ranar 7 ga Oktoban 2023.

 

Hare-haren na Isra’ila sun tsugunar da kusan dukkan jama’ar yankin da ci gaba da fuskantar mamayar da ta janyo karancin abinci, tsaftataccen ruwan sha, da magunguna.

 

Ƙoƙarin shiga tsakani da Amurka, Masar da Qatar ke jagoranta don a tsagaita wuta a Gaza da yin musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ya ci tura saboda yadda Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dakatar da yaƙin.

 

Yaki na tsawon shekara guda da yahudawan  sahyoniyya suke yi a Gaza ya yi ajalin mutane 42,000. Isra’ila na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi a Kotun Kasa da Kasa saboda ta’annatin da ta aikata a yankin, da ke da Falasdinawa sama da miliyan biyu.

 

A gefe guda, hare-haren Isra’ila a Lebanon tun daga 2023 zuwa yau sun yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 2,000 inda aka raba wasu milayan 1.2 da matsugunansu.

 

Mai rahoto;

Mustapha Garba usman.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 15, 2024 October 15, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Attajdid Attajdid February 8, 2026
Police Kills Five Suspected Kidnappers Arrest Others In Jigawa
Isra’ila Tana Luguden Wuta ta Sama a Beirut Bayan da take Fama da Wata Mummunar Tarjiya daga Dakarun Hezbollah
Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba 
Gwamnan Kano Eng.Abba Kabir Yusuf ya Kafa Majalisar Shura ta Jahar Kano 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?