Rahotonni daga Ƙaramar Hukumar Batsari a jihar Katsina na cewa an yi janaʼizar jamiʼan tsaron sa kai 3 na Katsina Community Watch Corps da gwamna Dikko Radda ya kafa.
Yan bindiga ne suka kashe jamiʼan sa kan bayan ɗauki ba daɗi da suka yi a garin Sayaya da ke Ƙaramar Hukumar Matazu.
Wadanda alʼamuran ya rutsa dasu ƴan garin Batsari ne, kuma tuni aka yi janaʼizarsu da yammacin Asabar a fadar Sarkin Ruma, Haikimin Batsari.
Daga cikin waɗanda yan bindigar suka hallaka har da Kwamanda Sunusi daya daga cikin manyan jagororin yan sa kan a yankin.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




