TATTALIN ARZIKI
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da Kara jarin Bankin manoma na kasa zuwa naira tiriliyan daya da digo biyar.
A wata sanarwa da ma’aikatar Noma ta kasa ta fitar tace wannan ne karon farko a tarihin Najeriya da Bankin ya samu adadin wannan kudi a matsayin jarin sa, Wanda ke nuni da fatan gwamnati na bunkasa harkokin Noma a kasar nan.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da ministan harkokin Noma da Samar da abinci Abubakar kyari ke bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta dukufa wajen aiwatar da manufofin Nima na kasa.
Manufofin sun Kunshi amfani da sabbin kayan noma da suka dace da zamani da Kuma sabuwar fasahar zamani tare da saukakawa manoma samun abubuwan da suke bukata na harkokin Noma.
Yace hakan zai Kara sanya sha’awar noma a tsakanin al’uma musamman ma matasa da Mata.
Awanni 48 da kara farashin litar Mai zuwa Naira Dari Tara da 55,, kamfanin Mai na kasa NNPCL ya sake rage farashin zuwa Naira Dari Tara a gidajen man da ke zama mallakin sa.
A wani bincike da jaridar punch ta gudanar ya nuna cewa tuni wasu gidajen man da ke mallakin NNPCL a Abuja suka canja farashin litar zuwa ga Sabon farashin na NNPCL.
Ragin na Naira 55 na zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu gidajen Man sun Kara farashin litar su zuwa naira Dari 9 da 55.




