By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Rikicin Gabas ta Tsakiya ya yi ƙamari Bayan Isra’ila ta Kai Hari a Iran
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Rikicin Gabas ta Tsakiya ya yi ƙamari Bayan Isra’ila ta Kai Hari a Iran
International News

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya yi ƙamari Bayan Isra’ila ta Kai Hari a Iran

Attajdid
Last updated: 2024/10/27 at 10:56 AM
Attajdid Published October 27, 2024
Share
SHARE

Isra’ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a “wuraren aikin soji” na Iran, kuma kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta tabbatar da jin ƙarar fashewar abubuwa sannan ta ce wasu daga cikin ƙarararrakin an ji su ne daga na’urorin kakkaɓo makamai da ke Tehran babban birnin ƙasar.

 

Babu bayani game da ɓarnar da hare-haren waɗanda aka kai da sanyin safiyar Asabar suka yi a Iran sai dai kafofin watsa labaran ƙasar sun rawaito cewa an “ji manya ƙararraki” a Tehran da yankuna da ke gefensa sakamakon hare-hare ta sama.

 

Rundunar sojojin Isra’ila ta bayyana hare-haren a matsayin na “yankan-shakku da aka kai kan wuraren aikin sojojin Iran.”

 

“Gwamnatin Iran da ƙawayenta sun riƙa kai hare-hare a Isra’ila tun 7 ga watan Oktoba 7 — a ɓangagori bakwai — ciki har da harin kai-tsaye daga ƙasar Iran,” a cewar wata sanarwa daga rundunar sojoji Isra’ila.

 

“Kamar kowace ƙasa mai cin gashin kanta a duniya, Ƙasar Isra’ila tana da damar mayar da martani.”

 

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta “shiga cikakken shiri” na kare kanta. Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasar Rear Admiral Daniel Hagari, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi kira ga al’ummar Isra’ila su “su sanya idanu kan abubuwan da ke wakana a kewayenku”.

 

Ba a kai hare-hare a tashoshin nukiliya ba, in ji kafar watsa labarai ta NBC News and ABC News , wadda ta ambato wani jami’in Isra’ila yana bayyana hakan.

 

Kamfanin dillancin labarai na Iran Farsya ce Isra’ila ta kai hari kan sansanonin soji da dama a kudanci da kudu maso yammacin Tehran.

 

Kamfanin dillancin labarai na Tasnimya ce an kai hari a sansanin sojojin Islamic Revolutionary Guard Corps amma ba a yi musu ɓarna ba.

 

Iran, wadda ta sha alwashin yin ramuwar gayya, ta ƙaddamar da hare-hare biyu da makamai masu linzami a Isra’ila a watannin da suka gabata a yayin da Isra’ila take ci gaba da yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza tun watan Oktoban 2023. Kazalika Isra’ila ta ƙaddamar da hare-hare na mamayar Lebanon.

 

Harin da Isra’ila ta kai wa Iran ranar Asabar na zuwa ne jin kaɗan bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya koma ƙasarsa bayan ya kammala balaguro a Gabas ta Tsakiya inda shi da wasu jami’an Amurka suka gargaɗi Isra’ila kada ta kai harin da zai ta’azzara rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da kuma tashoshin nukiliya.

 

A gefe guda, na’urorin Syria na kakkaɓo makamai sun “kakkaɓo” wani makami a kusa da Damascus da sanyin safiyar Asabar, a cewar kamfanin dillancin labarai na SANA.

 

“Na’urorinmu na kakkaɓo makamai ta sama sun tare wasu makamai a sararin samaniyar kusa da Damascus,” in ji wani saƙo da SANA ya wallafa a shafin Telegram bayan jin ƙarar “fashewa” a babban birnin Syria.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 27, 2024 October 27, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Zulum ya jaddada kudirinsa na sake tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa

Attajdid Attajdid November 27, 2024
Manhajojin Aika Sako a Matsayin Makaman ɓoye: Ko an yi amfani da WhatsApp a harin Isra’ila kan Iran?
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a sake fasalin tsarin ilimi don ya zo daidai da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban zamani
Birninkudu LG Empowers 170 Youth in To Agriculture
DA DUMI-DUMI: Iran Ta Fara Harba Makamai Masu Linzami Masu Tarin Yawa Cikin Isra’ila
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?