A cikin awanni 48 da suka gabata, Isra’ila ta kai hare-hare akalla hudu a cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a Kudancin Lebanon, inda ta jikkata ma’aikatan wanzar da zaman lafiya 4.
A watanni 12 da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kashe ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya akalla 220 da ke aiki a Gaza sannan sau dama jami’an Isra’ila suna shirga karya game da MDD, suna bayyana ta a matsayin “mai kyamar Yahudawa”.
At-tajdid News.




