Majiyar At-tajdid News ta yankin gabas ta tsakiya ta tabbatar da wasu rahotanni da suke nuni da irin hare-haren da aka kaiwa sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin sahayun
Wanna farmaki ya zone a daidai lokacin da duniya ke Cigaba da yin tofin Allahtsine ga takunkumin Yunwa da Israel tare da hadin guaiwar Amuruka suka sanyawa yankin Gaza.
Dakarun na Qassem sun kai haring kwanton bauna akan ayarin motocin dakon kayan aikin soja da na manfetur wadda hakan ya yi sanadiyyar konewar motocin tare da mutanen fake ciki.
Bayan haka mayakan mujahidin sun auka wa wani jirgin ruwan yahudawan sahyoniya na uku da makami mai linzami mai suna “Al-Yassin 105” a yankin Abasan Al-Kabira da ke gabashin birnin Khan Yunus a kudancin zirin Gaza. Rahotan sun bayyana yadda aka ringa binne motocin da kuma kashe wutar da jirage masu saukar ungulu na sauka domin kwashe wadanda suka Sami raunuka.
A wani hari da dakarun Qassam tare da hadin gwiwa da dakarun Al-Quds Brigades sun kai samame wajan aikawa da sakonni na ‘yan kama wuri zauna inda suka rusa wurin da ke birnin Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza ta hanyar yin amfani da wasu harsasai.
A wani rahoto da majiyar At-tajdid News ta samu daga yankin gabas ta tsakiya dakarun Al-Qassam Brigades sun kai hari kan wani jirgin yakin Isra’ila da ke dauke da nakiya masu yawa a yankin Abasan al-Kabira da ke gabashin Khan Yunis a kudancin zirin Gaza.
Dakarun Qassam sun fitar da rahoton akan wani hari da suka kai kan tankar Merkava da makami mai linzami a gabashin Jabalia na arewacin zirin Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




