Trump na son ganawa da Putin da zarar ya shirya hakan
Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna sha’awarsa ta gana da shugaban Rasha Vladimir Putin da zarar ya shirya hakan don ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.
A yayin ranar ƙarshe ta ziyararsa a Gabas ta Tsakiya, a wani taron majalisar kasuwanci a Hadaddiyar Daular Larabawa, Trump ya ce, “lokaci ya yi da za mu fara aiwatar da tattaunawar zamann lafiyar nan kuma za mu samu nasara.”
Ya jaddada cewa ba za a samu ci gaba mai ma’ana a tattaunawar zaman lafiyan ba sai an yi ganawar fuska da fuska da Putin.
Maganganun Trump na nuna fatan cewa ganawar kai tsaye zai taimaka wajen tura tattaunawar gaba.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




