Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fadi matsayarta akan batun yarjejenir tsagata wuta ta bakin Shugaba Biden dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ana bukatar hakan ya samu karbuwa daga bangarori daban-daban, ana bukatar sanya takaitaccen lokaci kan tafiyar da tattaunawar da ake yi a Doha dangane da Gaza inda aka rasa da yawan fararen hula da aka kashe a rikicin Gaza abin bakin ciki ne.Shima Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, ya ce muna cikin wani muhimmin lokaci na tabbatar da zaman lafiyar duniya kuma kwanaki masu zuwa na iya tabbatar da makomar gabas ta tsakiya sabo da halin da ake ciki a Gaza yana da muni kuma harin da aka kai a makarantar Al-Tabaeen ya nuna cewa Falasdinawa ba su da wani wuri mai aminci a yankin. Tattaunawar da ake yi wata dama ce ta tabbatar da tsagaita wuta nan take domin kare fararen hula a Gaza.
At-tajdid News.




