By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Haramta ƙungiyoyin Addini Fiye Da 40 a Kasar Rwanda.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > An Haramta ƙungiyoyin Addini Fiye Da 40 a Kasar Rwanda.
International News

An Haramta ƙungiyoyin Addini Fiye Da 40 a Kasar Rwanda.

Attajdid
Last updated: 2024/08/23 at 1:24 PM
Attajdid Published August 23, 2024
Share
SHARE

Gwamnatin Rwanda ta ɗauki matakin ne bayan ta rufe coci-coci fiye da 5,000 saboda gaza bin ƙa’idoji.

Gwamnatin Rwanda ta sanar da haramta ayyukan ƙungiyoyi 43 na addini a faɗin ƙasar daga ranar 28 ga watan Agusta, makonni bayan ta rufe dubban coci-coci da aka buɗe ba bisa ƙa’ida ba.

Wata wasiƙa da Ma’aikatar Kula da Ƙananan Hukumomi ta ƙasar ta fitar ta umarci dukkan shugabannin gundumomi su tabbatar da aiwatar da wannan mataki, tana mai cewa bincike ya gano cewa ƙungiyoyin suna karya dokoki.

Galibin coci-cocin da lamarin ya shafa na da alaƙa da ɗarikar Pentecostal, ciki har da Cocin Lutheran, mamba a Gamayyar Cocin Lutheran na Duniya wadda aka buɗe a Rwanda a shekarun 1990 domin ci gaba da ayyukan Jamusawa ‘yan mishan.

An sanar da haramta coci-cocin ne ranar Alhamis, makonni bayan hukumomi sun rufe fiye da coci 5,000 bisa zargin keta dokoki da jefa rayuwar masu ibada cikin hatsari.

Hukumomi sun ce kashi 59.3 na coci 13,000 da aka gudanar da bincike a kansu a ƙarshen watan Yuli an rufe su saboda gaza bin doka.Wannan ne karo na biyu da ake rufe coci-coci a ƙasar a shekarun baya bayan nan.

A shekara 2018, hukumomi a Rwanda sun rufe coci fiye da 700 da ake gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba.An umarci dukkan malaman coci su halarci wuraren bayar da horo kan addini kafin su buɗe coci kamar yadda doke ta tanada.

Gwamnati ta bai wa shugabannin coci-coci wa’adin shekaru biyar su aiwatar da matakan da ta tanada, sai dai rahotanni sun ce sau da dama sun gaza aiwatar da waɗannan matakai

At-tajdid News

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 23, 2024 August 23, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Infant Mortality Reduce By 26 % , Immunization rises To 90% In Jigawa– UNICEF

Attajdid Attajdid February 21, 2025
Sojojin Isra’ila: Sojoji da jami’ai 695 ne aka kashe tun farkon yakin da ake yi a Gaza.
Ukraine Says Russian Attacks Injure at Least 5, Cause Fires
FG, FMAN Supports 160,000 Wheat Farmers In Jigawa
Shekaru Biyun da Aka Shafe Ana Yaƙi Mafi Muni a Duniya  ya sa Sudan ta ɗaiɗaice
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?