An kai harin ne ranar Litinin da daddare a kan wani ɓangare na babban bututun man fetur da ke ƙauyen Bodo a ƙaramar hukumar Gokana ta Jihar Ribas.
Bayanai sun ce bututun yana cikin waɗanda suke fitar da ɗanyen mai daga Nijeriya zuwa ƙasashen waje.
Gidan talbijin na Channels Television ya ruwaito cewa mai yiwuwa an kai harin ne da gangan. Sai dai kawo yanzu hukumomi ba su ce komai ba game da lamarin.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




