Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin Mata sun fito zanga-zangar ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin kabilu Bachama da Chobo.
A lokacin zanga-zangar an ruwaito cewar mata bakwai ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata.
Shaidu sun ce sojoji sun buɗe musu wuta yayin da suke tare hanya, suna zargin rundunar da goyon bayan wata ƙabila.
Sai dai rundunar Sojin Najeriya ta musanta wannan zargi.
Ta ce dakarun sun yi artabu ne da wasu ‘yan bindiga a yankin, kuma ta ce mutuwar wasu mata biyu ya faru ne sakamakon buɗe wuta da ‘yan bindigar suka yi, ba wai sojoji suka harbe su ba.
Gwamnatin Jihar Adamawa, ta ayyana dokar hana fita na awa 24 a Lamurde domin daidaita al’amura da zaman lafiya.
A Numan, matan da suka sanya riga ɗauke da launin baƙi ne suka fara zanga-zangar a manyan tituna, inda suke neman yi wa waɗanda aka kashe adalci.
An riga an binne wasu daga cikin waɗanda suka rasu, lamarin da ya ƙara haifar da damuwa a tsakanin al’ummar yankin.
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin, Kwamoti Laori, ya yi Allah-wadai da kisan, inda ya ce ya kamata a gudanar da bincike mai zurfi.
Ya buƙaci hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace, tare da tabbatar da zaman lafiya ba tare da tauye haƙƙin ɗan Adam ba.
Mazauna yankin sun ce rigimar ta jefa mutane cikin tsoro, wanda hakan ya sa da dama suka tsare daga gidajensu.
At’tajdid News
Shugabannin al’umma a yankin, sun yi kira da a yi sulhu domin kaucewa ƙarin tashin hankali.




