- Isra’ila ta kai harin bam a tsakiyar birnin Beirut da sanyin safiyar Alhamis, inda ta kashe akalla mutane shida, bayan da sojojinta masu mamaya suka ga mafi munin rana a gagarumin artabun da ba su taba irinsa ba a fagen daga tsakaninsu da kungiyar Hezbollah ta Lebanon a cikin shekara guda.
- Shaidu sun ba da rahoton jin karar fashewar wani katon bam kuma wata majiyar tsaro ta ce Isra’ila ta kai hari kan wani gini da ke tsakiyar birnin Beirut a unguwar Bachoura da ke kusa da majalisar dokokin kasar, harin da Isra’ila ta kai a kusa da ofishin gwamnatin Lebanon.
- Akalla mutum shida ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata, in ji jami’an kiwon lafiya na kasar Lebanon.
- Wani hoto da ake yadawa a kafofin WhatsApp a kasar Lebanon ya nuna wani gini da ya lalace sosai tare da cin wuta a benensa na farko.
- Har ila yau, sun kai harin makami mai linzami uku a yankin kudancin Dahiyeh, inda aka kashe shugaban kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah a makon da ya gabata, an kuma ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi kamar yadda jami’an tsaron kasar Labanon suka sanar.
- Yankunan kudancin kasar sun fuskanci hare-hare sama da goma na Isra’ila a ranar Laraba.
- Hukumar kula da bala’o’i ta kasar Lebanon ta fada a baya cewa mutane 1,928 Isra’ila ta kashe a kasar tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
- Gwamnatin Amurka ta ce an kashe wani Ba’amurke dan asalin garin Dearborn a jihar Michigan, a kasar Labanon, inda abokin mutumin da makwabtansa suka ce an kashe shi ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama.
- Kakakin Fadar White House ya ce “Muna matukar bakin ciki da rasuwar Kamel Ahmad Jawad, kuma muna mika ta’aziyyarmu ga ‘yan uwansa da abokan arziki. Mutuwar tasa wata abar takaici ce, haka ma mutuwar fararen hula da dama a Lebanon.”
- Tun da farko dai, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, da aka tambaye shi game da rahotannin mutuwar wani Ba’amurke a Lebanon, ya ce: “A fahimtarmu ne cewa mazaunin kasar ne na dindindin bisa tsarin doka, ba wani Ba’amurke ba (wanda aka kashe a Lebanon) amma duk da haka muna mika ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa.”
- Yakin da Isra’ila ke yi a Zirin Gaza, wanda yanzu ya shiga kwana na 363, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,638. Bugu da ƙari, sama da mutane 1,928 ne suka mutu a wani munanan hare-haren da Isra’ila ta kai a Lebanon.
- At-tajdid News.
Leave a comment




