By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Sarkin Musulmi ya Bayyana Dalilin da ya sa Ake Ganin Kamar Sarakuna na Tsoron Gwamnoni
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Sarkin Musulmi ya Bayyana Dalilin da ya sa Ake Ganin Kamar Sarakuna na Tsoron Gwamnoni
News

Sarkin Musulmi ya Bayyana Dalilin da ya sa Ake Ganin Kamar Sarakuna na Tsoron Gwamnoni

Attajdid
Last updated: 2024/11/20 at 3:10 PM
Attajdid Published November 20, 2024
Share
SHARE

Sarkin Musulmi, Sa’ad Muhammad Abubakar II, ya musanta maganar da ke cewa sarakunan gargajiya na tsoron gwamnonin jihohi.

 

Ya bayyana cewa sarakunan gargajiya sun daɗe suna mulki tun kafin samun ’yancin kai a Najeriya, kuma suna da cikakkiyar fahimta game da ƙasa sama da gwamnonin jihohi.

 

Sarkin, ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawa kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya, a Abuja ranar Talata.

 

Ya mayar da martani ne, game da kalaman tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, wanda ya ce sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi.

 

Sarkin Musulmi ya ce, “Na ji wasu suna cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnonin jihohi. Wannan ba gaskiya ba ne.

 

“Sarakunan gargajiya kawai suna mutunta kansu da kuma mutunta gwamnonin, waɗanda ke da iko a jihohinsu. Ba wai tsoro ba ne.

 

“Idan wani abu ya faru, muna barinsa ga Allah Mai iko a kan komai. Muna karɓar duk wani sauyi da ya zo.

 

“Kafin a samu gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya sun riga sun fara mulki a wuraren da suka zama Najeriya tun daga 1914, kafin samun ’yancin kai a 1960.

 

“A matsayinmu na shugabannin gargajiya, muna da kusanci sosai da al’ummarmu saboda mun san buƙatunsu, kuma muna tare da su duk lokacin da wani abu ya faru.” KADAURA24.

 

Mai rahoto.

Balarabe.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid November 20, 2024 November 20, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

CBN Na Barazanar Rufe Kashi 95% na Kamfanonin Musayar Kuɗi

Attajdid Attajdid May 17, 2025
Isra’ila ta Kashe Mataimakin Shugaban Hukumar Kare Farar Hula ta Gaza
Biyan kudaden jarabawar NBAIS – NAPAIS ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano
Dakarun Al-Qassam Brigades Sun Kaiwa Sojojin Yahudawa Sahyoniyya Harin Kwantan Bauna
MALAM AMINU ALIYU GUSAU TAFSIR 2 GA RAMADAN 1443/2022
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?