Tana kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ta fitar da takardar sammacin Ministan Isra’ila mai tsattsauran ra’ayi Smotrich,furucin Smotrich ya fito da karara na daukar manufar kisan kare dangi a Gaza da kuma yin alfahari da haka.
A yayin wani jawabi da ya yi a ranar Litinin a wurin taron Katif kan na kasa da aka gudanar a garin Yad Binyamin,Ministan Kudi na Isra’ila Bezalel Smotrich ya ce “zai iya zama adalci da kuma halin kirki” a kashe mazauna Gaza miliyan 2 da yunwa har sai an dawo da mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su, amma “babu wanda zai bar mu a duniya.”
ministan mai tsattsauran ra’ayi ya ce kamata ya yi Isra’ila ta karbe ikon raba kayan agaji a cikin Gaza, ya kuma yi ikirarin cewa Hamas ce ke da ikon rarrabawa a cikin yankin. Yana cewa “Ba zai yiwu ba a cikin duniya a yau a hanmu yaki kuma babu wani a duniya da zai hanamu mu jefa yunwa da kishirwa ga ‘yan kasa miliyan biyu, ko da yake hakan yana iya zama adalci da kuma ɗabi’a har sai sun dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji shi, ya kara da cewa, da Isra’ila ta mallaki iko rabon kayan agaji maimakon Hamas, da yanzu yakin ya kare kuma da wadanda aka yi garkuwa da su sun dawo.
Ya ci gaba da cewa “Ba za ku iya yakar Hamas ta hannu daya kuma ku ba su taimako ta hannu daya yana kuma cewa Kudinsa ne, man fetur dinsa ne, hakama ikon farar hula na zirin Gaza in ji shi da Isra’ila ce ke da iko kan taimakon da ke shiga Gaza ba kungiyoyin agaji ne ke da alhakin rarrabawaba”.
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




