Rundunar Kataib al-Qassam, reshen soja na ƙungiyar Hamas, ta ce mayakanta sun kai hari a safiyar jiya Laraba kan motocin soja biyu na Isra’ila irin Hummer a kudancin Gaza.
An ce an harbi motocin da roka mai ƙarfi nau’in Yasin 105, lamarin da ya jawo mutuwar wasu sojojin Isra’ila da raunuka ga wasu.
Rahotanni sun bayyana cewa an ga jiragen sama na soja suna sauka domin ɗaukar waɗanda suka ji rauni, a kusa da asibitin Gura al-Lut a birnin Khan Younis.
A wani harin daban, a jiya Talata, mayakan Al-Qassam sun yi ruwan bama-bamai kan taron sojojin Isra’ila a yankin al-Maqousi, arewa maso yammacin Gaza.
Haka kuma, rundunar ta tabbatar da cewa ranar biyar ga Oktoba, ta tarwatsa wata tankin “Merkava” ta Isra’ila da nakiya mai ƙarfi a yankin al-Barada‘i, kusa da titin Street 10 a kudancin birnin Gaza.
Al-Qassam ta ce hare-haren suna ci gaba, yayin da aka hango jiragen Isra’ila suna zagaye a sararin Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




