‘Kuɗin cizo sun hana mu kwana a gidajenmu’
A Harare, babban birnin ƙasar Zimbabwe, hukumomi na fafutikar ganin sun yaƙi ƙananan ƙwarin nan masu shan jinin ɗan’adam, wato kuɗin cizo.
Mazauna unguwar Mbare da ke babban birnin sun shaida wa shirin BBC na Focus on Africa Podcast cewa sun gaji da rayuwar ƙawanya da kuɗaɗen cizo suka musu.
“Yanzu ba ma iya bacci a gidajenmu, da zarar yamma ta yi za ka ji yara na ta ihu saboda kuɗin cizo sun addabe su, ba mu iya ziyaratar ƴan’uwanmu haka nan su ma ba su iya ziyartar mu, duk saboda kuɗin cizo,” in ji wata mata da ke zaune a unguwar.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS👆




