By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900
News

Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900

Attajdid
Last updated: 2025/05/28 at 11:11 AM
Attajdid Published May 28, 2025
Share
SHARE

Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta ci tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da wasu mutum biyar tarar Naira miliyan 900.

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna a ranar Talata ta ci tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da karin wasu mutum biyar tarar Naira miliyan 900.

Kotun dai ta ci tarar tsohon Gwamnan kan laifin kamawa tare da tsare dattawan kabilar Adara da ke jihar a shekara ta 2019.

Da take zartar da hukuncin a ranar Talata, Alkalin kotun, Mai Shari’a Hauwa’u Buhari, ta amince da bukatar Awemi Dio Maisamari da Karin wasu dattawan kabilar ta Adara su takwas wadanda aka kama bayan kisan basarakensu, Dr Raphael Maiwada Galadima.

Kotun dai ta yi fatali da da’awar wadanda ake kara kan cewa ba ta da hurumin sauraron karar, inda duk da haka ta yanke hukuncin.

An dai gurfanar da El-Rufa’i ne a kashin kansa ba a matsayin Gwamna ba, inda kotun ta ce ta same shi da laifi kan bayar da umarnin yin kamen.

Lauyar masu shigar da karar, Gloria Mabeiam Ballason Esq, ta bayyana hukuncin a matsayin wani babbar nasara kan masu amfani da kujerar mulkin ta hanyar da ba ta dace ba.

An dai kama tare da tsare dattawan na kabilar Adara ne a shakara ta 2019 yayin wani taro da El-Rufa’i ya gayyace su a shekara ta 2019, jim kadan bayan sacewa da kuma kisan da aka yi wa basaraken.

A yayin taron, rahotanni sun ce El-Rufa’i y aba jami’an tsaro umarnin kama Maisamari, wanda shi ne shugaban Kungiyar Ci Gaban Adara, inda ya bayyana shi a matsayin barazanar tsaro a yankin Kajuru.

Dattawan da aka kama dai sun hada da tsohon Kwamishina kuma tsohon jami’in dan sanda, inda aka tsare su har na tsawon watanni, kafin daga bisani babban lauyan gwamnati ya bayar da umarnin sakin su tun da ba a tuhume su a kotu ba.

To sai dai lauyoyin wadanda ake kara sun ki su ce uffan a kan hukuncin kotun.

Mai rahoto
Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid May 28, 2025 May 28, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Uncategorized

BUSINESS  CBN SELLS DOLLAR TO ACCESS, FBN, FIDELITY, 23 Other Banks, DISQUALIFIES SIX (Full List)

Attajdid Attajdid August 12, 2024
AMBALIYAR RUWA A GARIN MAIDUGURI
Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone
Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 31 Tare Da Rusa Gida 5,000 a Jihar Kano
Duk da Dauki da Ake Kaiwa Gaza Ana Cigaba da Rasa Rayuka Sakamakon Takunkumin Yunwa da Isra’ila da Kawarta Amurka Suka Kakabawa Yankin Gaza 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?