By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Taliban ta Halarci Taron MDD Karo na Farko a Azabaijan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Gwamnatin Taliban ta Halarci Taron MDD Karo na Farko a Azabaijan
International News

Gwamnatin Taliban ta Halarci Taron MDD Karo na Farko a Azabaijan

Attajdid
Last updated: 2024/11/12 at 6:11 AM
Attajdid Published November 12, 2024
Share
SHARE

Shekarar 2024 na kan hanyar kafa tarihin ɗumamar yanayi, wanda ke ƙara bayyana gaggawa ga muhawarar da ta kawo rarrabuwar kai game da matakin yaki da tasirin sauyin yanayi a kasashe matalauta.

 

Hamed Safi, daga dama, mamban tawagar Afganistran, na magana da abokin aikinsa a yayin taron COP29 a Baku, a ranar 11 ga Nuwamba, 2024, ranar da aka fara taron sauyin yanayi na MDD na 2024.

 

Gwamnatin Taliban ta halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a karon farko tun bayan karbar ragamar Afghanistan a 2021, in ji hukumar kula da muhalli ta kasar.

 

An fara gudanar da taron na COP29 a ranar Litinin a Azabaijan, kuma daya daga cikin muhimman tattaunawa da za a yi shi ne kan Taliban.

 

Ana sa ran sun sami matsayin ‘yan kallo a wajen taron.

 

Hukumar Kula da Kare Muhalli ta Kasa ta sanar ta shafinta na X cewa jami’anta sun halarci taron da ake gudanarwa a Baku.

 

Matiul Haq Khalis, shugaban hukumar, ya ce tawagar za ta yi amfani da taron wajen karfafa hadin kai da kasashen duniya kan kare muhalli da rikicin sauyin yanayi, sannan za su bayyana bukatar Afganistan na samun damar amfani da kudadenta na sauyin yanayi, sannan su tattauna kan kokarin rage tasiri.

 

Kwararru sun fada wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa rikicin sauyin yanayi ya janyo illoli da dama kan Afganistan, ya kawo kalubale manya saboda yankin da kasar take da rashin daukar kwararar matakan yaki da illar.

 

“Rikicin sauyin yanayi ya janyo dumamar yanayi, wanda ke rage ruwan da ake samu don amfani, tare da janyo fari, wanda ke illata harkokin noma” in ji Hayatullah Mashwani, farfesa kan kimiyyar yanayi da muhalli a Jami’ar Kabul.

 

“Raguwar ruwan da ake da shi da yawaitar fari na yi babbar barazana ga ayyukan noma, wanda ke kawo karancin abinci da kalubalen ji dadin rayuwa.”

 

A watan Agusta, kungiyar agaji ta kasa da kasa ‘Save The Children’ ta fitar da wani rahoto da ke cewa Afganistan ce kasa ta shida a duniya mafi rauni da ke illatuwa da tasirin sauyin yanayi, kuma 25 daga lardunanta 34 na fuskantar matsanancin fari, wanda ke shafar sama da rabin jama’ar kasar.

 

Afganistan kuma na da yara mafi yawan yara da illar sauyin yanayi ya raba da matsugunansu ya zuwa karshen 2023.

 

Farfesa Abid Arabzai, na Jami’ar Kabul ya ce taron na sauyin yanayi zai taimaka wajen samun tallafin kasa da kasa da kudade don magance kalubalen sauyin yanayi a Afganistan.

 

“Afganistan na iya fayyace matakai da kokarin da take yi na yaki da sauyin yanayi ga kasashen duniya,tana sake inganta darajarta a matakin kasa da kasa,” in ji Arabzai.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 12, 2024 November 12, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Fafaroma Francis ya Nemi Ayi Bincika ko Isra’ila na aikata Kisan Kiyashi a Gaza

Attajdid Attajdid November 21, 2024
Hisbah Aikin Allah: Gwamna Amadu, Gwamnan Addini.
MAAIKATAN JINYA SUN JANYE YAJIN AIKIN YAU
Gov Yusuf emerges SME Governor of year 2024
MUHIMMAN ABUBUWAN DA SHUGABA TINUBU YA BAYYANAWA ‘YAN NIGERIA AKN ZANGA-ZANGAR
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?