Rundunar sojin ƙasar Nijeriya ta ce ta kashe gomman mayaƙan Boko Haram/ISWAP a Mallam Fatori da kuma Buratai duka a jihar Bornon Nijeriya da sanyin safiyar ranar Alhamis.
Duk da cewa sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ba ta ba da ƙarin bayani ba game da yadda ta fatattaki ‘yan ta’addan, wani rahoton kafar Zagazola Makama da aka fi sani da ba ta rahoto kan lamurran tsaro a yankin ya ce kashe-kashen Malam Fatari sun auku ne a lokacin da ‘yan ta’addan wajen 150 suka kai hari a sansanin ‘yan gudun hijira na Malam Fatori.
Rahoton na Zagazola ya bayyana cewa, bayan an yi bata-kashi na tsawon kimanin sa’o’i huɗu, yan ta’addan sun shiga wani ɓangare na sansanin.
Sai dai kuma wasu sojoji sun sake haɗuwa inda suka tinkari ‘yan ta’addan kuma ƙarfin bindigogin sojojin ya sa ‘yan ta’addan suka ja da baya, in ji rahoton na Zagazaola Makama.
Cikin ‘yan makonnin nan dai ‘yan Boko Haram/ISWAP suna ta matsa kaimi wajen kai hare-hare kan sansanonin sojojin Nijeriya a jihohin Borno da Yobe inda suke amfani da jirage mara matuƙa wajen kai hare-haren nasu.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




