By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ba zamu taɓa ajiye makami ba, har sai an samar da ƙasar Falasɗinu-HAMAS
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Ba zamu taɓa ajiye makami ba, har sai an samar da ƙasar Falasɗinu-HAMAS
International News

Ba zamu taɓa ajiye makami ba, har sai an samar da ƙasar Falasɗinu-HAMAS

Attajdid
Last updated: 2025/08/02 at 5:13 PM
Attajdid Published August 2, 2025
Share
SHARE

 

Ƙungiyar Hamas ta sake jadadda matakin ta na cewa ba zata taɓa ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da yantacciyar ƙasar Falaɗinu a yankin gabas ta tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin ƙullawa baya.

 

 

A halin da ake ciki yanzu haka ana wata tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba tsakanin Isra’ila da Hamas don ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60, da kuma sakin mutanen da ke riƙe a hannun ɓangarorin biyu.

 

A Talatar da ta gabata ne ƙasahen Qatar da Masar suka sanar da matakin ƙasashen Saudi Arabiya da Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasdinu, don tabbatar da dawamammen zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

 

To amma ƙasashen sun ce hakan zata yiwu ne kawai idan har Hamas ta amince da ajiye makamai ga mahukuntan Faladinu da ke Ramallah.

 

A wata sanarwa da Hamas ɗin ta fitar ta ce bazata taɓa ajiye makamai ba, har sai ta tabbatar da samun ƴancin kan Falasɗinawa, da kuma ayyana birnin Ƙudus a matsayin babban birni.

 

Wannan ba shine karon farko da Hamas ke bayyana hakan a matsayin hanya ɗaya tilo ta ajiye makami ba, yayinda ita kuma Isra’ila ke cewa zata yi kowacce irin tattaunawa da Hamas ne bayan sun amince da ajiye makami.

 

A makon da ya gabata Prime ministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya ce ba shakka samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu, shimfida hanya ne na rusa Isra’ila don haka ba zai taɓa aminta da hakan ba, kuma dole ne sha’anin tsaron yankunan Falasɗinu ya kasance ƙarƙashin ikon ƙasar sa.

 

Da yake chachakar matakin ƙasashen Burtaniya, Canada da kuma Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasɗinu biyo bayan halin da Isra’ila ta jefa al’ummar Gaza, ya ce wannan abu ne da Hamas ta janyo.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

At’tajdid News

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 2, 2025 August 2, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Distributes Foods, Cash Reliefs To 15,775 Flood Victims Households

Attajdid Attajdid September 11, 2024
Ministan Kula da Albarkatun teku Adegboyega Oyetola ya sha Alwashin rage dogaron Nigeria akan shigo da kifi daga kasashen ketare ta hanyar habaka noman kifi a cikin gida tare da kyautata fasahar kiwon kifi a fadin Nigeria.
KUNGIYAR HAMAS TA ZABI YAHYA SINWAR A MATSAYIN SABON SHUGABANTA BAYAN SHAHADAR ISMAIL HANIYYAH.
October 22, 2024
Nijeriya ta Sake Tsunduma Cikin  Gagarumin Rashin Wutar Lantarki
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?