TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (3).
MANHAJAR TATTAUNAWA.
A wannan silsila ba tarihin Tajdidin Shehu na ke nufin in kawo ba tiryan – tiryan. Ina son ne in sha Allahu in amsa wasu tambayoyi a cikin gaba guda biyu:
A . GABA TA FARKO: A nan zamu yi kokarin amsa tambaya guda biyu in sha Allahu kamar haka:
1 . Menene amfanin Tajdidin Shehu ga kasar Hausa da Arewacin Najeriya a addinance da siyasance da abunda ya shafi yanayin zamantakewa da tattalin arziki?
2 . Wadanne matsaloli ne za su shafi arewacin Najeriya a addinance da siyasance da abunda ya shafi yanayin zamantakewa da tattalin arziki, sakamakon haifar da rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Fulani?
B . GABA TA BIYU: A nan zamu yi kokarin bayanin wasu shubuhohi da masu son kawo fitinar kabilanci tsakanin Hausawa da Fulani a arewacin Najeriya suke amfani da su, dangane da abunda ya shafi Tajdidin Shehu Dan Fodiyo, wadanda suka hada da:
1 . Yanayin zamantakewar Fulani da sauran kabilu a “Biladus Sudan” kafin Tajdidin Shehu;
2 . Musulunci a Biladus Sudan kafin Tajdidin Shehu;
3 . Me ake nufi da “Tajdidi”?; An yi Tajdidi a Biladus Sudan kafin na Shehu Dan Fodiyo?;
4 . Shehu Dan Fodiyo yana da manufofin neman mulki a cikin Tajdidin sa?;
5 . Tajdidin Shehu Dan Fodiyo ta’addanci ne?;
6 . Tajdidin Shehu Dan Fodiyo kabilanci ne? Ya aka yi mulkin Sarakunan kasar Hausa da kewaye ya koma hannun Fulani?;
7 . Me ake nufi da “Hausa-Fulani”?
Da kuma wasu tambayoyi da za su iya tasowa a cikin tattaunawa in sha Allahu.
Modibbon Gu
sau.
14/11/1446H
12/05/2025M.




