By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > Books & Journal > TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU
Books & Journal

TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU

Attajdid
Last updated: 2025/05/17 at 4:40 AM
Attajdid Published May 17, 2025
Share
SHARE

TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (2).

 

DAIDAITA FAHIMTA:

 

Kafin mu tsunduma a cikin munakashar da zamu yi yana da kyau mu daidaita fahimtar jama’a kan wasu manyan shubuhohi da ke tattare da wannan tattaunawa.

 

Daga cikin abubuwan da tarihi ingantacce ya tabbatar akwai cewar:

 

1 . Shehu Dan Fodiyo ba shine ya yo hijira daga wani wurin ya sauka kasar Hausa ya kulla yakin da su ba. Ba shine ya jagoranto Fulani zuwa kasar Hausa ba. Shehu haifaffen dan kasar Gobir ne. Kakannin sa sun yi shekaru a kalla dari biyu da hansin (250) zuwa dari uku (300) da tarewa kasar Gobir kafin a haife shi. Don haka Shehu ba bako ba ne a Gobir, bai san ko ina ba banda kasar Hausa. Su ma Sarakunan Gobir da na sauran kasashen Hausa wadanda Shehu ya yi lokaci da su ba su dauki Fulani baki ba, sun dai dauki cewar su ma talakawansu ne, kamar sauran Hausawa. A cikin dukkan littafan tarihin jihadin Shehu babu inda aka taba ruwaito cewar Sarakunan kasar Hausa na lokacin suna kiran Fulani da “Baki”, sai dai ko su ce masu “‘yan Fulani”, ko kuma su ce masu “mabiyan Usman”, saboda wanda ya yi a kalla shekaru dari uku ga wuri ya wuce a ce masa bako. Kalmar cewar “Baki” sun zo sun yi tawaye sun karbe mulki, masu son kawo fitina a yau ne suka zo da ita. Zamu yi karin bayani game da yawan shekarun da Hausawa suka riga Fulani da su, da zuwa kasar da bayan zuwansu ake kiranta “kasar Hausa” in sha Allahu.

 

2 . Shehu Tajdidin Musulunci ya yi. Shehu malami ne mai Da’awa, wanda dukkan matakan da ya dauka tun daga wa’azi har zuwa yaki da kafa daula sai da ya rubuta a kalla littafi daya domin bayyana manufofinsa da hujjojinsa na Addinin Musulunci na daukar wannan matakin. Dukkan wadannan littafai da ya rubuta da wadanda mabiyan sa suka rubuta duk suna nan a kasuwa, kowa zai iya samun su har zuwa yau din nan. Maganar Tajdidi magana ce ta ilimi da hujjojin Addini. Ba dole ne wani ya yarda da hujjojin Shehu ba, amma hakan ba zai ba kowa damar ya kautar masa da manufofin sa ba zuwa wani abu daban, kamar a ce manufar ta’addanci ya ke da ita, ko ta neman mulki ko ta kabilanci, ba tare da kawo ko wace irin hujja ba in banda shaci fadi.

 

3 . A yau Tajdidin Shehu yana da shekaru dari biyu da ashirin da daya (221) da wucewa. Bayan shi ma har turawa sun shigo sun rusa daular da ya samar, sun yi mulki na a kalla shekaru sittin (60) sun wuce da tsawon shekaru sittin da biyar (65). A Najeriyar yau, da Nijar din yau, ba daular Shehu ce ke mulki ba, sannan Bafulatani ko da shi Sarkin gargajiya ne ba bu abunda ya ke iya hana Bahaushe ko Bazabarme ko Buzu samu don kawai su ba Fulani bane. To tambaya a nan ita ce: su masu yunkurin raba kan Fulani da Hausawa a Najeriya da Nijar, me suke son cimmawa? In banda sarautar gargajiya wane abu ne Fulani suka tare ma wasunsu daga samu? Idan sarautar gargajiyar ta komai hannun Hausawa wane ci gaba ne za ta kawo muna a matsayin mu na musulmi, ko ‘yan arewacin Najeriya, ko ‘yan Najeriyar, ko ‘yan Nijar, ko ma a matsayinmu na Hausawa?

 

Modibbon Gusau.

12/11/1446

H.

10/05/2025M.

You Might Also Like

TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (5). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU

TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (4). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU

TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (3). SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU

TAJADIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (1) SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU

SULHUN TSAGAITA WUTA TSAKANIN HAMAS DA ISRA’ILA – WA YA CIMMA MANUFOFIN SA, WAYE BAI YI BA?

Attajdid May 17, 2025 May 17, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Video

Bayani kan Masjidul Aqsah tare da Malam Aminu Aliyu Gusau.

Attajdid Attajdid August 3, 2024
Amnesty, Da Likitocin England Sun Bukaci Israel Ta Saki Maaikatan Lafiya Palestine 95
Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca
Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Baranta akan Zargin Da Ake Mata Na Rashin Bai Wa Daurarru Ishesshen Abinci.
JUST IN: Tension as fire guts Emir Sanusi’s palace in Kano
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?