By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: AN KAI HARI  YANKIN TILLABERI NA JAMHURIYAR NIJAR DA YAKE IYAKA DA MALI DA BURKINA FASO.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > AN KAI HARI  YANKIN TILLABERI NA JAMHURIYAR NIJAR DA YAKE IYAKA DA MALI DA BURKINA FASO.
International News

AN KAI HARI  YANKIN TILLABERI NA JAMHURIYAR NIJAR DA YAKE IYAKA DA MALI DA BURKINA FASO.

Attajdid
Last updated: 2024/08/15 at 9:02 AM
Attajdid Published August 15, 2024
Share
SHARE

Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da ƙungiyar IS da Al-Qaeda.An kashe fararen-hula 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu hare-haren ta’addanci da aka kai a ƙauyukan yammacin Nijar da ke kusa da iyakar Burkina Faso a farkon makon nan, in ji sanarwar da rundunar sojin ƙasar ta fitar a yammacin jiya Laraba.

“A yankin Mehana, ‘yan ta’adda sun kai munanan hare-hare da dama kan fararen-hular da ba su da kariya, inda aka samu mummunar asara,” in ji sanarwar, inda aka ce an kashe mutum 14 a wata rana da ba a tantance ba, lamarin da ya biyo bayan mutuwar aƙalla wani farar-hula guda a ranar Talata duk a yanki ɗaya.

Mehana na daga cikin yankuna shida da aka kai hari a yankin Tillaberi na Jamhuriyar Nijar mai iyaka da Mali da Burkina Faso kuma ya zama maɓoyar mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da kungiyar IS da Al-Qaeda.

Ƙungiyoyin ‘yan ta’adda na yawan kai wa fararen hula hari a Mehana, lamarin da ke raba mutane da dama da muhallansu.Har ila yau, a yankin Tillaberi a ranar Talata, wani farar-hula ɗaya ya mutu, wasu uku kuma suka jikkata, a wani ƙazamin rikici da ya ɓarke tsakanin sashen binciken sojoji da ‘yan ta’adda a kusa da garin Chatoumane, in ji rundunar.

“Jami’an tsaro sun dauki matakin da ya dace, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama,” in ji sojojin.Kasar Nijar dai na ƙarƙashin jagorancin shugabanin sojoji ne da suka ƙwace mulki a watan Yuli, inda suka ce sun yi hakan ne saboda yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa.Nijar na kuma na fuskantar tashin hankali daga mayaƙan Boko Haram da kuma abokan hamayyarsu na IS da ke yankin yammacin Afirka daga yankin Diffa da ke kudu maso gabashin Nijeriya.A cewar Acled, wata cibiya mai bin diddigin rikice-rikice, masu iƙirarin jihadi sun kashe fararen-hula da sojoji kusan 1,500 a cikin shekarar da ta gabata a Nijar, idan aka kwatanta da 650 a cikin shekara zuwa Yuli 2023.TRT AFRIKA

At-tajdid News 

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 15, 2024 August 15, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Dr Kwankwaso Na Gab Da Komawa APC

Attajdid Attajdid July 22, 2025
Jigawa First Lady Urges Northern Women to Embrace Entrepreneurship for Self-Reliance
POSITION OF JAMA’ATUT TAJDIDIL ISLAMY (J.T.I) ON THE UP COMINGNATION WIDE DEMONSTRATION.
Flood Displaced Over Ome Million People In Borno StateOver one million people were displaced by devastating flood hits Maiduguri and some part of Borno state.
Dakarun Isra’ila Sun Kai Hari a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Mawasi Khan Yunis
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?