Taron me taken “Aikin dake gaban kowane musulmi”
Taron da aka gabatar a ranar Lahadi a dakin taro dake makarantar sakadare ta maza dake kofar na’isa.
Wannan taro ne da ya kara karfafa shugabanni da mabiya na kungiyar Jama’atu Tajdidil Islamy yankin Gwale kano.
An kira wannan taro da suna; waye ni kuma me yake gabana a matsayin na na musulmi.
Taron ya sami halartar wasu daga jagororin wannan kungiya na sama watau kano ta tsakiya.
An gabatar da taro ga iyaye da matasa harma da yara kanan. Haka an samu fa’ida da kuma samun fahimta sosai duba da malaman da sukayi bayani.
Masu bayani sune:
Malam Adamu Ajingi
Malam umar Shehu tsakuwa
Malam isma’el Habib
Malam Aminu sani mai nagge
Malam Ahmad Diso
Da sauransu.
Allah ya amfana da wanda suka ji abubuwan da aka gabatar a wurin ya kuma basu ikon yi wa addini aiki da gaskiya.
Mai rahoto;
Muhammad Nuru Adam.
At-tajdid News.





