Gwamnan addini, His Excellency Dr. Ahmad Aliyu Sokoto FCNA ya dawo da aikin Hisbah a Jihar Sokoto, bayan da tsohuwar gwamnatin baya ta soke aikin.
Kasancewar Sokoto cibiya ce ta addinin Musulunci kuma cibiya ce ta Daular Usmaniyya, tun bayan gwamnati baba Alu, Jihar Sokoto ba ta sake samun gwamna mai addini ba kamar wannan lokaci na Amadun Alu. Gwamnan ya dawo da aikin Hisbah ne bisa jagorancin Malam Usman Abdullahi Jatau inda kuma shugaban Hisbah na Jihar Kano Malam Daurawa ya kaddamar da ita.
▪︎Maigirma gwamna ya dawo da aikin Hisbah ne domin karfafa aiyukan gyaran tarbiyar al’umma a Jihar Sokoto, bisa koyarwar addinin Musulunci.
▪︎Domin tallafawa hukumar wajen gudanar da aiyukanta, an samar mata da motoci da babura da kuma wadataccen ofis. Kari akan wannan kuma, nan ba da dadewa ba, za a bude ofisoshin hukumar Hisbah na kananan hukumomi in sha Allah.
“Na bukaci sabuwar hukumar Hisban da ta tuna cewa, cin zarafin mutane da ba su ji ba kuma ba su gani ba, baya cikin dalilan da suka sa aka kafa ta. Na kuma umarci jami’an hukumar da su yi aiki bisa doron dokar da ta kafa hukumar, su kuma tabbatar da cewa aiyukansu ba su ci karo da kundin tsarin mulkin kasa ba.
Kafa hukumar Hisbah ba shi da manufar maye gurbin hukumomin tsaro da ake da su, sai dai za su tallafi harkar tsaro ne domin kare lafiya da dukiyoyin al’ummar Jihar Sokoto.
Jami’an hukumar za su yi aiki ne bisa doka, wacce ta basu damar yin kame, daga bisani su kuma mika wanda ake zargi ga jami’an ‘Yansanda domin gurfanar da shi a gaban kotun shari’ar musulunci.
Za mu cigaba da bibiyar aiyukan hukumar domin tabbatar da cewa sun bi shimfidaddun dokoki da ka’idoji wajen gudanar da aiyukansu.” – Dr. Ahmad Aliyu Sokoto FCNA
Shugaban AYSAS, Bashar Attahiru ya yi kira ga al’ummar Jihar Sokoto da su ba hukumar da jami’anta hadin kai wajen sauke nauyin da ya rataya akansu.
At’tajdid News




