By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi Sauye-Sauye a Majalisar Zartarwa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi Sauye-Sauye a Majalisar Zartarwa
News

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi Sauye-Sauye a Majalisar Zartarwa

Attajdid
Last updated: 2024/10/25 at 3:21 AM
Attajdid Published October 25, 2024
Share
SHARE

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sallami wasu ministoci biyar tare da naɗa wasu sabbi guda bakwai a ranar Laraba.

 

Kazalika ya sauyawa ministoci 10 ma’aikatun da suke aiki, yayin da sabbin ministocin da aka naɗa kuma za su jira tabbatarwa daga Majalisar Dattijan Ƙasar.

 

Shugaban Ƙasar ya kori Ministar Mata Uju-Ken Ohanenye da Ministar Yawon Bude Ido Lola Ade-John da Ministan Ilimi Tahir Mamman da Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane Abdullahi Gwarzo da Ministar Ci Gaban Matasa Jamila Ibrahim.

 

Sai kuma ya ba da sunayen Bianca Odumegu-Ojukwu a matsayin Ministar Harkokin Waje, yayin da aka ba da sunan Nentawe Yilwatda a matsayin Ministar Jinƙai da Rage Talauci, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin Betta Edu wacce aka dakatar tun tuni.

 

A sanarwra da Fadar Shugaban Ƙasar ta fitar, an kuma ga sunan Maigari Dingyadi a matsayin Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Jumoke Oduwole Ministar Masana’antu da Idi Maiha Ministan sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa Kiwo, da Yusuf Ata a matsayin Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane sai kuma Suwaiba Amhad a matsayin Ƙaramar Ministar Ilimi.

 

Sai kuma Shugaba Tinubu ya sanar da Shehu Dikko a matsayin sabon shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa.

 

Sannan Sunday Akin Dare ya zama sabon Mai Baiwa Shugaban Kasar Shawara na Musamman a kan Harkokin Sadarwar Jama’a wanda zai dinga aiki daga Ma’aikatar Watsa Labarai.

 

Shugaban ya gode wa ministocin da aka sallama din a yayin taron majalisar zartarwa da kuma yi musu fatan alheri a rayuwarsu ta gaba.

 

Sai kuma ya nemi sabbin ministocin da ma wadanda aka sauyawa ma’aikatu da su yi aiki tuƙuru don yi wa ƙasa hidima.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid October 25, 2024 October 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Yahudawan Sahyoniyya Sun Kashe Saban Shugaban Hezbollah

Attajdid Attajdid October 25, 2024
NG-CARES Distributes Motorcycles to Facilitators in Jigawa
World Contraceptive Day: Jigawa Women Advocate More Supply Of Contraceptives, FP Services
Aljeriya ta Buƙaci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka
YAN BINDIGA SUNKAI HARI UNGUWAR LADO DA KARO DAKE MALUNFASHI
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?