YAN BINDIGA SUNKAI HARI UNGUWAR LADO DA KARO DAKE MALUNFASHI
Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tarwatsa wasu yan bindiga suka kai hari Unguwar Lado da Karo a Ƙaramar Hukumar Malunfashi.
Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar a Asabar din nan.
Sanarwar ta ce yayin arangamar yan sanda sun hallaka ƙasurgumin dan bindigar nan Audu Kushin na ƙauyen Tsamiyar Maigoro.
Sai dai yan bindigar sun jikkata mutane 5 da suka yi kokarin garkuwa da su ciki har da mai unguwa.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu




