By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Aljeriya ta Buƙaci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Aljeriya ta Buƙaci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka
International News

Aljeriya ta Buƙaci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka

Attajdid
Last updated: 2024/12/30 at 4:57 PM
Attajdid Published December 30, 2024
Share
SHARE

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya ƙaddamar da wata sabuwar caccaka kan Faransa dangane da tasirin da mulkin mallakar da ƙasar ta yi wa Aljeriya.

 

Ya caccaki Faransar ne a lokacin da ya gudanar da jawabi ga ƙasar a gaban duka majalisun ƙasar inda ya gabatar da irin nasarorin da ya samu a wa’adinsa na farko na shugabancin ƙasar tsakanin 2019 zuwa 2024 da kuma ƙara fitar da manufofinsa a wa’adinsa na biyu wanda ya fara a wata Satumba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito.

 

Tebboune ya bayyana cewa Aljeriya na so Faransa ta amince da irin laifukan da ta aikata a lokacin mulkin mallaka tsakanin 1830 zuwa 1962, inda ta jaddada cewa ƙasar ba ta buƙatar wata diyya.

 

“Muna neman dawo da mutuncin kakanninmu,” in ji shi

 

‘Yan Aljeriya da aka kashe

 

“Adadin ‘yan Aljeriya da aka kashe a tsawon shekara 132 na mulkin mallaka ya kai miliyan 5.6, kuma babu adadin kuɗin da za a biya da za su kasance diyyar ko da mutum ɗaya da aka kashe a lokacin gwagwarmayar,” in ji shi.

 

Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin Aljeriya da Faransa, lamarin da ya kai ga janye jakadan Aljeriya tare da kiran jakadan Faransa.

 

Hukumomin Aljeriya sun danganta wannan tashin hankalin da “mugayen ayyuka da jami’an leken asirin Faransa na kasashen waje suka aikata a kasar Aljeriya.”

 

Tebboune ya kuma tuno da irin ta’asar da sojojin Faransa ‘yan mulkin mallaka suka aikata, musamman a karkashin Janar Thomas Robert Bugeaud, gwamnan-Janar na Aljeriya daga 1841-1847, wanda ya bayyana a matsayin “kisan kare dangi.”

 

Ya bayyana cewa har yanzu Faransa na riƙe da kawunan ƙwarangal fiye da 500 na ‘yan Aljeriya waɗanda ta fille wa kai a ƙarni na 19 inda aka kai kawunan Paris.

 

“Mun yi ƙoƙarin karɓo kawuna 24 kacal,” kamar yadda ya bayyana.TRT Africa Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid December 30, 2024 December 30, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

GOV. LAWAL DISBURSES OVER N11 BILLION GRANTS FOR GIRLS’ EDUCATION PROJECT IN ZAMFARA

Attajdid Attajdid September 11, 2024
AN SAMU CIMA MATSAYA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA KARIM LAMIDO
Majiya daga Isra’ila:Ta tabbatar da an kai sojoji 10 zuwa 15 zuwa asibitoci
Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Wadata Nigeria Da Makamashin Mara Illa
Rasha ta hallaka mutum 12 a wani sabon hari a Ukraine
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?