By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Sojojin Isra’ila na Sahyoniyya Sun Kai Hari Cikin Gidajan Fararan Hula a Gaza da Lebanon.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Sojojin Isra’ila na Sahyoniyya Sun Kai Hari Cikin Gidajan Fararan Hula a Gaza da Lebanon.
International News

Sojojin Isra’ila na Sahyoniyya Sun Kai Hari Cikin Gidajan Fararan Hula a Gaza da Lebanon.

Attajdid
Last updated: 2024/11/10 at 4:31 PM
Attajdid Published November 10, 2024
Share
SHARE

Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce mutum 30 da suka hada da kananan yara 13 ne suka mutu a wasu hare-hare biyu da Isra’ila ta kai kan wasu gidaje biyu a arewacin Falasɗinu.

 

Harin na farko wanda aka kai shi da safiyar Lahadi ya faɗa ne a wani gida da ke Jabalia da ke arewacin Gaza, inda ya kashe aƙalla mutum 25 daga ciki har da yara 13 tare da jikkata sama da mutum 30, in ji hukumar kare farar hular.

 

Wani harin kuma ya faɗa ne a unguwar Sabra da ke birnin Gaza inda mutum biyar suka rasu, wasu da dama kuma sun ɓata bayan harin.

 

Hukumar ta kara da cewa, har yanzu akwai fararen hula da dama a karkashin baraguzan ginin..

 

Akalla mutum 27 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a gabashi da kudancin kasar Lebanon, in ji ma’aikatar lafiya.

 

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, wani harin da Isra’ila ta kai a gabashin garin Aalamat da ke gundumar Jbeil ya kashe mutum 20 ciki har da yara uku.

 

Ta kara da cewa an jikkata wasu shida a harin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto domin neman wadanda suka tsira.

 

Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza wanda a yanzu ya shiga kwana na 399 ya kashe akalla Falasdinawa 43,552 da jikkata 102,765, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra’ila ta kashe mutum 3,136 tun Oktoban bara. TRT Afarka Hausa.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 10, 2024 November 10, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Kotu Ta Tasa keyar Wani  Alƙalin Bogi Gidan Gyaran Hali a Kano

Attajdid Attajdid September 6, 2024
Saƙon da Mahamat Deby ya ce mu kawo wa Tinubu game da yaƙi da Boko Haram – Nuhu Ribadu
Zamfara State Governor, His Excellency Dauda Lawal, will perform the inauguration of the Zamfara State Council of Ulama today the 30th of July, 2024 at the Government House chamber in Gusau.
Irin Jerin Hare-haren da Dakarun Mukawama Suke Kaiwa Yahudawan Sahyoniya a Gaza 
Yankin Nijar yana Fama da Hare-haren ‘Yan Ta’adda
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?