By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Katsina ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantun Koyon Aikin Lafiya Masu Zaman Kansu
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin Katsina ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantun Koyon Aikin Lafiya Masu Zaman Kansu
News

Gwamnatin Katsina ta Bayar da Umarnin Rufe Makarantun Koyon Aikin Lafiya Masu Zaman Kansu

Attajdid
Last updated: 2024/10/22 at 9:31 PM
Attajdid Published October 22, 2024
Share
SHARE

Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya Dikko Radda ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun koyon kiwon lafiya masu zaman kansu da ke faɗin jihar tare da soke lasisinsu.

 

Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin lafiya, Umar Mammada, ya sanar da wannan mataki ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Katsina.

 

Gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan wani bincike da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta gudanar da ya nuna makarantun ba su da inganci sannan da dama daga cikinsu ba su da rijista, lamarin da ya tayar da hankalin gwamnati.

 

Mammada ya ce a shekarun baya-bayan, jihar ta Katsina ta samu ƙaruwar makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya masu zaman kansu, waɗanda da dama daga cikinsu ba su da rajista kuma ba su da inganci.

 

“Ko da yake mun san muhimmiyar rawar da makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu suke takawa wajen tabbatar da lafiyar al’umma, amma yana da muhimmanci mu tabbatar da ingancinsu domin kare lafiyar al’ummarmu,” in ji Mammada.

 

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta samar da tsari mai inganci da zai tabbatar da ƙwarewar irin waɗannan makarantu kafin a ba su damar ci gaba da horar da masu neman ilimin kiwon lafiya.

 

Jihar Katsina na cikin jihohin Nijeriya da ke fuskantar ƙalubale a fannin kiwon lafiya da tsaro kuma gwamnatin jihar ta sha alwashin shawo kan matsalolin, abin da ya sa masana suka yaba mata kan ɗaukar wannan mataki.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid October 22, 2024 October 22, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Awards N336. 6 Billion Contracts For Capital Projects

Attajdid Attajdid September 11, 2024
Ɗantakarar Hamayya ya Kayar da Shugaban ƙasa Mai-ci a Somalilan
Israeli lawmaker urges world to act to prevent ‘genocide’ in West Bank
AN KASHE ISMA’IL HANIYEH SHUGABAN OFISHIN SIYASA NA KUNGIYAR HAMAS.
Turkish Airlines ya Koma Zırga-zırga Zuwa Syria Bayan Shafe Shekaru 11 da Dakatarwa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?