By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ɗantakarar Hamayya ya Kayar da Shugaban ƙasa Mai-ci a Somalilan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Ɗantakarar Hamayya ya Kayar da Shugaban ƙasa Mai-ci a Somalilan
International News

Ɗantakarar Hamayya ya Kayar da Shugaban ƙasa Mai-ci a Somalilan

Attajdid
Last updated: 2024/11/19 at 1:35 PM
Attajdid Published November 19, 2024
Share
SHARE

Ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya a yankin Somaliland da ya ayyana cin gashin-kansa daga Somalia, Abdirahman Mohamed Abdillahi (Irro) ya kayar da shugaban ƙasar mai-ci, Muse Bihi Abdi, a zaɓen da aka yi, kamar yadda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar a yau Talata.

 

Jagoran jam’iyyar hamayya, Waddani – Abdirahman, ya samu kashi 63.92 cikin ɗari yayin da Shugaba Bihi ya ci kashi 34.81 cikin ɗari, na ƙuri’u kamar yadda hukumar zaɓen ta sanar.

 

An haifi Abdirahman Irro a Hargaisa, babban birnin ƙasar ta Somaliland, ranar 29, ga watan Afirilun 1955, inda ya yi makarantar elimantare a Somalia, kuma daga nan ya je kwaleji a Amurka, har ya yi digiri na biyu a fannin kula da harkokin kasuwanci.

 

Irro ya yi aikin diflomasiyya a ofishin jakadancin Somalia a Moscow, inda ya fara aikin diflomasiyya a ma’aikatar harkokin wajen Somalia a 1981.

 

A lokacin yaƙin basasa a 1991 na Somalia ya kasance muƙaddashin jakadan Somalia a tsohuwar Tarayyar Sobiyet.

 

Daga baya ya tafi Finlad inda ya je ya zauna da iyalinsa a can har ya samu takardar zama ɗan ƙasar.

 

Irro ya fara shiga siyasar Somaliland a 2002, a jam’iyyar UCID.

 

Ya kasance shugaban majalisar dokokin Somaliland tsawon shekara 12 daga 2005.

 

Irro ya kafa jam’iyyar Waddani a 2012, inda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2017, amma ya sha kaye a hannun Muse Bihi Abdi.

 

A wannan shekarar kuma ya sake yin takarar inda ya yi nasarar kayar da shugaban mai-ci.

 

Somaliland ta kasance ƙarƙashin mulkin kanta da ta ayyana tun bayan da ta sanar da yankewa daga Somalia a 1991, sai dai ba ƙasar da ta amince da ita a matsayin ƙasa har yanzu, wanda hakan ya taƙaita mata samun kuɗaɗe daga waje da kuma haifar da ƙalubale ga al’ummarta miliyan shida wajen tafiye-tafiye.

 

Mai Rahoto;

Mujahid Muhammad Tasiu.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 19, 2024 November 19, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International NewsNews

WANENE JABOTINSKY WANDA NETANYAHU YAKE BI  KUMA YA AJIYE TAKOBINSA?

Attajdid Attajdid September 18, 2024
Ko gwamnoni duka za su koma APC ba zai hana mu kayar da Tinubu a 2027 ba — Babachir
December 12, 2024
Ambaliya ta kashe mutane da dama a Jihar Neja
Sojojin Isra’ila Sun Canja Salan Yaki da ‘Yan Houthis
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?