By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: NIJERIYA TA ZARGI WANI KAMFANIN KASAR CHINA DA KOKARIN KWACE KADARORIN GWAMNATI.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > NIJERIYA TA ZARGI WANI KAMFANIN KASAR CHINA DA KOKARIN KWACE KADARORIN GWAMNATI.
News

NIJERIYA TA ZARGI WANI KAMFANIN KASAR CHINA DA KOKARIN KWACE KADARORIN GWAMNATI.

Attajdid
Last updated: 2024/08/16 at 2:02 PM
Attajdid Published August 16, 2024
Share
SHARE

Nijeriya ta zargi wani kamfani na kasar China da ƙoƙarin ƙwace kadarorin gwamnatin tarayya ba bisa ƙa’ida ba bayan wata taƙaddama da jihar Ogun.Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce a ranar 15 ga watan Agusta, 2024, tana aiki tare da jihar Ogun domin warware rikicin da kuma kare kadarorin kasar daga ƙwacewa.

Fadar Shugaban Nijeriya da Gwamnatin Nijeriya ta zargi wani kamfanin ƙasar China da yunƙurin ƙwace kadarorinta a ƙasashen ƙetare ciki har da jiragen Shugaban Ƙasa, kamar yadda kakakin shugaban ƙasar ya bayyana a ranar Alhamis.Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar, Bayo Onanuga, ya ce Kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Ltd yana amfani da “hanyar da ba ta dace ba” wajen ƙoƙarin ƙwace kadarorin gwamnatin Nijeriya, duk da cewa ba shi da wata alaƙa ta kwangila da gwamnatin tarayyar.

Kamfanin Zhongshan bai mayar da martani ba nan-take.Taƙaddamar dai ta samo asali ne daga wata kwangilar da Zhongshan ya ƙulla da jihar Ogun ta kudu maso yammacin Nijeriya a shekarar 2007, ta samar da yankin kasuwanci marar shinge, wanda aka soke a shekarar 2015.’Babu ƙaƙƙarfar hujja’ Onanuga ya ce lokacin da aka soke kwantiragin jihar Ogun a shekarar 2015, abin da Zhongshan ya yi na aikin bai wuce gina katanga ba a filin da aka keɓe domin gina yankin kasuwanci marar shingen. “Zhongshan ba shi da ƙwaƙƙwarar hujjar da zai buƙaci gwamnatin jihar Ogun ta biya shi bisa hujjar kwangilar da aka ƙulla tsakanin kamfanin da gwamnatin jihar a shekarar 2007 don gina yankin kasuwanci marar shinge,” in ji Onanuga.

Gwamnatin Nijeriyar dai ta ce ba ta cikin wannan kwangilar, kuma Zhongshan ya gabatar da wasu hujjoji da ba daidai ba a gaban kotuna a Birtaniya, da Amurka, da kuma Faransa, inda kotu ta ce a biya shi dala miliyan 60 a matsayin diyya.Nijeriya ta ƙi biyan waɗannan kuɗaɗe, in ji Onanuga.

Kadarorin da ba su da kariyaOnanuga ya ce, Zhongshan ya samu umarni biyu daga wata kotun Faransa a watan Maris da Agusta na ƙwace kadarorin Nijeriya, ciki har da jiragen Shugaban Ƙasa da ake kula da su a Faransa. Ya ce waɗannan kadarorin ba su da kariya daga ayyukan shari’a na ƙasashen waje.

Gwamnatin Nijeriya na aiki tare da jihar Ogun domin shawo kan rikicin da kuma kare kadarorin ƙasar da aka ƙwace,

TRT AFRIKA, in ji Onanuga.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid August 16, 2024 August 16, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Ramadan Feeding: Beyond Welfarism

Attajdid Attajdid March 6, 2025
Anti- Hardship : Police Arrests 212 Protestants, In Jigawa.
Zan ƙara Bawa ‘Yan Nijeriya da Kamfanoni Hanyoyin Samun Bashi-Tinubu
APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed
ANA CIGABA DA SHIRYE-SHIRYEN TSAGAITA WUTAR YAKIN DAKE FARUWA A GAZA.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?