By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Zan ƙara Bawa ‘Yan Nijeriya da Kamfanoni Hanyoyin Samun Bashi-Tinubu
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Zan ƙara Bawa ‘Yan Nijeriya da Kamfanoni Hanyoyin Samun Bashi-Tinubu
News

Zan ƙara Bawa ‘Yan Nijeriya da Kamfanoni Hanyoyin Samun Bashi-Tinubu

Attajdid
Last updated: 2025/01/02 at 11:25 AM
Attajdid Published January 2, 2025
Share
SHARE

Shugaban Nijeriya ya ce gwamnatinsa za ta rage hauhawar farashi a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka noma da tallafa wa masana’antu don haɗa muhimman magunguna a cikin gida.

 

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta ƙara buɗe hanyoyin samun bashi ga ‘yan ƙasar da ma masana’antu domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar a cikin sabuwar shekarar 2025.

 

A jawabinsa ga ‘yan ƙasar wanda ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi wannan ne ta hanyar kafa wani kamfani da zai kasance asusun tabbatar da biyan bashi na ƙasa wato National Credit Gurantee Company domin rage hatsarin ba da bashi ga bankuna da kamfanoni.

 

“Kamfanin da ake sa ran zai fara aiki kafin tsakiyar shekara zai kasance na haɗin-gwiwa ne tsakanin ma’aikatun gwamnati kamar bankin masana’antu da hukumar ba da bashi ga mutane (Nigerian Consumer Credit Corporation) da kamfanin zuba jari na Nijeriya da ma’aikatar kuɗi ta Nijeriya da ‘yan kasuwa da kuma hukumomin ƙasa da-ƙasa,” in ji shugaban.

 

Alkaluma sun nuna tattalin arzikin Nijeriya na bunkasa da jan hankalin masu zuba jari

 

“Wannan matakin zai ƙarfafa aminci a tsarin kuɗin ƙasar tare da ƙara hanyar samun bashi da kuma tallafa wa waɗanda ba su cika samun dama ba irin su mata da matasa. Zai kawo ci-gaba da farfaɗo da masana’antu da kuma inganta rayuwar al’umarmu,” a cewar Tinubu.

 

Kazalika shugaban ya ce gwamnati za ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa hauhawar farashi ta ragu daga kashi 34.6 cikin 100 zuwa kashi 15 a cikin 100 a shekarar 2025 ta hanyar haɓaka harkar noma tare da inganta haɗa muhimman magunguna a cikin gida.

 

Shugaban, da ya nemi ‘yan ƙasar su goya masa baya wajen tabbatar da cewa tattalin arziƙin ƙasar ya kai na dala tiriliyon ɗaya, ya ce dole ‘yan ƙasar su inganta biyayyarsu ga ƙasar domin ta iya cim ma muradunta.

 

“Gaskiyar ‘yan ƙasa da kuma amincewarsu da ƙasar na da muhimmanci wajen nasarar Muradun Sabon Fata,” in ji shugaban wanda ya ce gwamnati za ta mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da halayen da suka kamata ‘yan ƙasar su kasance suna da su.

 

Ya ƙara da cewa shi zai ƙaddamar da wani shrin wayar da kan jama’a a shekarar 2025 wanda zai mayar da hankali kan kishin ƙasa da kuma son ƙasa ta yadda waɗanda suke gwamnati da sauran ‘yan ƙasa za su yarda da juna tare da haɗa kai. TRT Africa Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid January 2, 2025 January 2, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

A Leap Forward: Governor Namadi’s Vision for Jigawa’s Youth

Attajdid Attajdid April 23, 2025
Triumph Furious As Dollar Crashes In Market Reserves
Hon. Yazeed Shehu Danfulani: A Shining Example of Selfless Leadership and Philanthropy.
An Haramta ƙungiyoyin Addini Fiye Da 40 a Kasar Rwanda.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a sake fasalin tsarin ilimi don ya zo daidai da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban zamani
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?