Al-Qassam ta kai harin kwantan bauna a ranar Juma’a data gabata sun sami nasarar kai harin kan tankokin yaki na yahudawan Sahayoniya guda 3 na Merkava 4 dauke da harsashi 105 na Al-Yassin a yayin harin sun kai hari kan wani shingen sojoji su 7 daga wani gida da harsashi na “TBG”, kuma sun kashe su tare da raunata wasun su.
Sun kai kuma wani hari ga wata buldoza na soja na D9 tare da harsashin Tandom cikin gaggawa rundunar bada agaji ta kai dauki Sanadiyar tashin gobara.
At-tajdid News ta samu wani daga Al-zeera Syria da yake nuna cewa ‘yan adawar Siriya masu dauke da makamai sun hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a wani hannin kuma Rasha tana tuntubar dukkan bangarorin ‘yan adawar.
Kwamandan Sashen Ayyuka na ‘Yan adawar Siriya Ahmed Al-Sharaa ya bayyana Nasarar da aka samu nasara ce ga dukkan Siriyawa kamar yadda Al Jazeera Syria ta kawo.
‘Yan adawar Siriya suna kara samun goyanbaya musamman daga bangaran Ahalul sunnah, Muftin Oman ya ce “Muna taya al’ummar Siriya ‘yan uwa maza da mata murnar yadda suka gudanar da juyan mulki ba tare da zubar da jini ba, kuma akwai darasi a kan abin da ya faru, kuma akwai darasi abin daukar darasin mai hankali shi ne ke ganewa”.
Mai rahoto:
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




