Wani babban jigon siyasar Hamas, Khalil al Hayya, ya tabbatar da kashe shugaban kungiyar, Yahya Sinwar.
Al Hayya a cikin wata sanarwa ta bidiyo, ya nanata matsayin kungiyar gwagwarmayar Falasdinu na cewa ba za ta sako mutanen da ta yi garkuwa da su a harin da ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023 a Isra’ila ba har sai an tsagaita wuta a yakin Gaza na shekara daya.
“Wadancan fursunonin ba za su dawo gare ku ba kafin a kawo ƙarshen wuce gona da irin da kuke yi a Gaza da kuma janye yaƙin,” in ji shi.
Yaƙin da mahukuntan Isra’ila suka kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,438.
A gefe guda, hare-haren da Isra’ila ta ƙaɗdamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,411 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.
TRT Afarka Hausa.
Mai rahoto;
Mustapha G. Usman.
At-tajdid News




