By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Turkish Airlines ya Koma Zırga-zırga Zuwa Syria Bayan Shafe Shekaru 11 da Dakatarwa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Turkish Airlines ya Koma Zırga-zırga Zuwa Syria Bayan Shafe Shekaru 11 da Dakatarwa
International News

Turkish Airlines ya Koma Zırga-zırga Zuwa Syria Bayan Shafe Shekaru 11 da Dakatarwa

Attajdid
Last updated: 2025/01/23 at 7:14 PM
Attajdid Published January 23, 2025
Share
SHARE

Kamfanin jiragen saman Turkish Airlines ya ce ya koma da zirga-zirgar jiragensa zuwa ƙasar Syria bayan shafe tsawon shekaru 11 da dakatarwa.

 

A ranar Alhamis ne jirgin farko ya tashi daga Istanbul zuwa Damascus, yayin da ‘yan Syria da dama suka yi ta nuna farin cikinsu da komawa ƙasarsu bayan shafe shekaru da dama suna gudun hijira.

 

Aƙalla mutane 350 ne suka samu damar shiga jirgin farko, inda wasu daga cikinsu ke ɗauke da tutar ƙasar Syria.

 

Ɗaya daga cikin fasinjojin mai suna Fatma Zehra ta shaida wa manema labarai cewa ta zo Turkiyya ne tun tana ‘yar shekara 2 a duniya, kuma a yanzu tana matuƙar farin cikin komawa tare da danginta zuwa ƙasarsu ta asali inda aka haife ta.

 

”Ban taɓa ganin ƙasata ba, ina matukar farin cikin ganinta a karon farko. Za mu tashi ne daga Damascus zuwa Aleppo. Zan ga kakata a can,” a cewar Zehra, wadda a yanzu take da shekaru 14.

 

Kimanin ‘yan Syria miliyan 4 ne suka samu mafaka a maƙwabciyar ƙasar Turkiyya a lokacin yaƙin basasar.

 

A cewar wani fasinjan jirgin, Ahmet Kiraz, ya zo Turkiyya ne a shekarar 2012, inda ya gina rayuwarsa ta hanyar karatu da samun aiki, kuma bai taɓa tunanin komawa Syria ba.

 

”Mun yi tsammanin ba za mu taɓa komawa ba,” in ji shi. Amma a lokaci da damar ta zo, mun yi farin ciki sosai. Zan koma ƙasata a jirgin farko, ji nake yi kamar ina mafarki,” a cewar Kiraz.

TRT African Hausa.

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid January 23, 2025 January 23, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Dakarun Isra’ila Sun Sace ƙarin Falasɗinawa Bakwai

Attajdid Attajdid January 23, 2025
YAN BINDIGA SUNKAI HARI UNGUWAR LADO DA KARO DAKE MALUNFASHI
Kasar China Tana Yunkurin Rusa Wani Masallaci Tare Muzgunawa Musulman Kasar
BAZAWARA TA KONE KANTA A JIGAWA.
Stakeholders Moves To Promote Gender Equality In Criminal Justice Administration In Jigawa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?