Kungiyar Hezbollah ta tabbatar da cewa Isra’ila ta kashe Hashem Safieddine, wanda ake ganin shi ya gaji shugabanta da aka kashe Hassan Nasrallah, a wani harin da ta kai, ba tare da bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar wadda ke samun goyon bayan Iran ta ce “Muna jimamin…shugaban majalisar zartarwar kungiyar Hezbollah, babban malami Sayyed Hashem Safieddine,” inda ta ƙara da cewa wani harin wuce gona da iri na Yahudawa masu tsananin aƙidar son kafa ƙasar Isra’ila ne ya kashe shi tare da wasu mayaƙan kungiyar Hezbollah.
At-tajdid News.




