☆Dakarun Falasdinawa sun yi wa wata runduna ta musamman ta Isra’ila kawanya da suka shiga tare da kutsawa cikin wani gida a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, kuma ana ta samun kazamin fada a wurin a yanzu.
☆An harba makamai masu linzami 15 daga Gaza zuwa yankunan ‘yan mamaya.
☆A arewacin Gaza da sauran yankunan yara na mutuwa sakamakon tashin bama-bamai da yunwa.

☆Sanarwar da ministocin harkokin wajen G7 suka fitar: “Muna nuna matukar damuwarmu game da tsananin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya. Tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya na barazanar haifar da barkewar rikici a yankin gabas ta tsakiya.
☆Wani gagarumin farmakin da dakarun Falasdinawa suka kai a Rafah da ke kudancin zirin Gaza.
☆ ‘Yan mamaya na kwashe sojojinsu da suka mutu da wadanda suka jikkata.
☆Majiyar kiwon lafiya ta Aljazeera: Ta ce Shahidai 18 aka samu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a yankuna daban-daban a zirin Gaza tun da safiyar yau.
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




