UNICEF:
Yara a kasashe da dama a Gabas ta tsakiya suna fuskantar wani mummunan lamari a yau fiye da kowane lokaci duk wani tashin hankali a yankin zai haifar da mummunan sakamako da zai kai jefa rayuwar yara cikin hatsari muna kira ga dukkanin bangarori da su gaggauta yin amfani da ka’idoji. Sunyi kira da aringa kulawa da kare fararen hula.
A daidai lokacin da aka tsinci gawar wani yaro da ‘yar uwarsa kwanaki uku bayan sun yi shahada a Gaza.Kusan yara 15,000 ne aka kashe a yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas, in ji MDD. Adadin yaran da suka bace ko kuma suka rabu da iyalansu a Gaza sakamakon yakin na iya kaiwa 21,000, a cewar kungiyar agaji ta Save the Children. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce a kalla Falasdinawa 34,568 ne suka mutu sannan wasu 77,765 suka jikkata a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba.
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




