Rasha ba da gaske take ba kan maganar sulhu – Zelensky.
Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ba da gaske take ba kan tattaunawar zaman lafiya, bayan da Vladimir Putin ya ki halartar zaman shiga tsakani a Turkiya da nufin tsagaita wuta a yaƙin Ukraine.
Shugaban na Ukraine ya bayyana hakan ne bayan ganawa da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Ankara.
A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Santanbul da ke ƙasar Turkiyya, amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar.
Tun a jiya ne mista Zelensky ya isa babban birnin Turkiyya, Ankara, domin tattaunawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan sannan ya halarci taron.
Zelensky zai yi tattaunawar zaman lafiya da Vladimir Putin na Rasha a Istanbul amma ya yanke shawarar tura tawaga a maimakon hakan bayan nuna rashin amincewa da Putin.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




